Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-09 20:29:53    
Gwamnatin kasar Sin tana kokarin ceto ma'aikatan Sin da aka yi garkuwa da su a Nijeriya

cri

A ran 9 ga wata a birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Liu Jianchao ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana kokarin ceto ma'aikatan Sin 5 da aka yi garkuwa da su a Nijeriya, a halin yanzu kuma, wadannan Sinawa 5 suna lami lafiya.

Mr Liu ya gargada Sinawa da ke da bukatar aiki ko yawon shakatawa ko karatu a kasashen waje da su mai da hankali sosai a kan lafiyarsu, kuma ya ce, kamata ya yi su kara tuntubar ofishin jakadancin kasar Sin a kasashen waje a yayin da suka gamu da matsaloli.(Danladi)