Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-09 16:08:22    
Babbar ganuwa ta sashen Jinshanling

cri

An fara gina babbar ganuwa ta sashen Jinshanling a karni na 6. An gina hasumiyoyin yin kalla guda 67 na salo iri daban daban a kan babbar ganuwa ta wannan sashe, akwai ratar misalin mita 150 a tsakanin hasumiyoyin yin kallo 2. A zamanin daular Ming ta kasar Sin wato daga shekara ta 1368 zuwa ta 1644, wani janar na kasar Sin ya inganta babbar ganuwa ta sashen Jinshanling saboda dalilin tsaron kai. Ko da yake ganuwa na da inganci, kuma hasumiyoyin yin kallo na da tsayi, inda sojoji suka iya yin kallo cikin sauki, amma tudu da gangara na wannan wuri ya sanya babbar ganuwa ta sashen Jinshanling ta kasance wuri mai hadari, akwai saukin kai hari, amma akwai wahalar kare kai.

Sifar babbar ganuwa ta sashen Jinshanling ta yi kama da wani babban dodo irin na kasar Sin, wato dabbar Long a Sinance, ta kuma yi wa kanta hanya mai kwane-kwane a kan tsaunuka.

Masu sha'awar daukar hotuna sun fi son daukar hoto kan babbar ganuwa ta sashen Jinshanling. An kiyaye babbar ganuwa tun daga sashen Simatai na Beijing zuwa sashen Jinshanling na lardin Hebei yadda ya kamata, shi ya sa masu yawon shakatawa da yawa daga kasashen waje sun kai ziyara a nan. An ce, yawan mutanen ketare da suka yi yawon shakatawa a nan ya fi na gida. Haka kuma, bayan da suka kai wa babbar ganuwa ta sashen Jinshanling ziyara, to, ba za su so yin ziyara ga sauran sassan babbar ganuwa ba. Har zuwa yanzu mutane sun iya ganin ni'imtattun wurare masu kyan gani a babbar ganuwa ta sashen Jinshanling kamar yadda aka gani a zamanin daular Ming.

Babbar ganuwa ta kasar Sin ta zama wadda ta ga tarihin sarakunan kasar Sin a idonta, ta kuma nuna hikimar jama'ar Sin masu kuzari, da kuma kyawawan al'adun kasar Sin da kuma tarihinsa.(Tasallah)