Guijie suna ne da fararen hula na Beijing suke kira wani titin da ke shiyyar Dongzhimen ta gundumar Dongcheng ta Beijing, inda dakunan cin abinci da yawa ke bude kofofinsu. Babban halin musamman nasa shi ne ko kusan dukan dakunan cin abinci suna yin awoyi 24 suna sayar da abinci, sa'an nan kuma, cinikinsu ya yi kyau da dare, in an kwatanta da rana. Madam Li Xiaojun, mai jagorancin masu yawon shakatawa na ofishin harkokin yawon shakatawa na matasa na kasar Sin ta yi bayani kan dalilin da ya sa ana kiransa da titin Guijie da cewa, 'Ma'anar Gui a Sinance ita ce dodo, Jie ita ce titi. An ce, da can titin nan kasuwa ce inda 'yan kasuwa masu sayar da kayayyakin zaman yau da kullun da masu sayar da kayan lambu da 'ya'yan itatuwa suka sami rinjaye, yawancinsu su kan yi ciniki a daddare, su kan koma gida da sassafe a ko wace rana, 'yan kasuwa sun yi amfani da fitilun kananzir da dare, a lokacin nan mutane sun kira wannan kasuwa kasuwar Gui, wato kasuwar dodo. Daga baya hukumar gundumar Dongcheng ta Beijing ta bunkasa titin nan a matsayin titin cin abinci, ta samar da wani katon mutum-mutumin kwaf na shan giya a kofar titin, ta kuma kyautata sunansa zuwa titin Guijie, lafazinsu sun yi daidai, amma ma'anarsu sun sha bamban.'
Ana sayar da abinci mai dadin ci iri daban daban a wannan titi mai tsawon misalin kilomita 1.5, inda dakunan cin abinci misalin 200 suke sayar da abinci irin na wurare daban daban. An rataye manyan jajayen fitilu fiye da 500 da kuma kananan jajayen fitilu fiye da dubu daya a gefunan hanyar da kuma a bakin kofofin dakunan cin abinci, sun hada al'adun gargajiya na kasar Sin da zaman rayuwa na zamani na dare gaba daya. Ko a lokacin zafi ko kuma a lokacin hunturu, a kan sami rububin mutane kaiwa da dawowa da kuma motoci a cunkushe a nan da dare.
Dakin cin abinci mai suna Hua Jia Yi Yuan dakin cin abinci ne mafi girma a kan wannan titi a yanzu. Ya bude rassan dakunan cin abinci biyu a titin na arewa, wadanda dukansu rukunin gidaje na musamman na Beijing. An shimfida hanyoyi masu kwane-kwane a cikin wadannan dakunan cin abinci 2, haka kuma an bai wa mutane teburori da kujeru masu alfarma domin cin abinci. Tsoffin gine-gine sun nuna salon Beijing na gargajiya. Darektan wannan dakin cin abinci Jiang Jingjian ya bayyana cewa,'Da can wani babban janar ya zauna a nan. Daga baya mun yi kwaskwarima, mun raya su zuwa dakunan cin abinci. Amma ba mu yi watsi da wasu halayen musamman na rukunin gidaje ba. A lokacin hunturu, mun dumama dakunan ta hanyar musamman na rukunin gidaje. Ban da wannan kuma, mun bai wa mutanen kasashen waje takardun sunayen abinci a Turance. Muna fatan abokanmu na kasashen waje da ke cin abinci a nan za su fahimci kyawawan al'adun cin abinci na gargajiya na kasar Sin.'
Abincin da ake samarwa a dakin cin abinci na Hua Jia Yi Yuan sun sha bamban da na sauran dakunan cin abinci, Kuku-kukun wannan dakin cin abinci sun mai da hankulansu kan hada al'adun cin abinci na kasar Sin da na kasashen yamma gaba daya.
In an tabo magana kan titin Guijie, da farko mutane sun tuna da abincin ruwa na lobsterlings da aka dafa su da man girke da barkono da yaji da yawa a ko wane dakin cin abinci a kan wannan titi. Wadannan dafassun lobsterlings launinsu jar wur, kuma na da yaji da dadin ci. A galibi dai mutane sun zo titin Guijie don cin irin wannan abincin ruwa mai matukar dadin ci.
A shekarun nan da suka wuce, an yi ta bunkasawa da yin kwaskwarima kan titin Guijie, an fadada wasu shahararrun dakunan cin abinci, shi ya sa an samar da yanayi mai kyau a fannin cin abinci.
Bayan da aka yi kwaskwarima, wasu dakunan cin abinci masu halin musamman na kasashen yamma sun bude kofofinsu a titin Guijie, amma mutanen kasashen waje da suka zo daga nesa sun fi son cin abinci irin na kasar Sin. Kurt Kutzler, wanda ya zo daga kasar Denmark, ya nuna babban yabo ga gasassun agwagi da aka yi musu kwaskwarima, yana ganin cewa, gasassun agwagi da ake sayarwa a nan ya fi cancanci mutanen kasashen waje. Ya ce, 'A ganina, gasassun agwagi na da dadin ci a nan, sa'an nan kuma, ina mamaki sosai saboda namijin kokarin da aka bayar wajen gasa agwagi. Ina sha'awa cin gasassun agwagi tare da wasu sauran abinci na musamman. Musamman ma wajibi ne ko wane mutum, wanda bai taba ci gasassun agwagi a da ba, ya duba yadda saura suka ci kafin ya bude bakinsa. A takaice dai, gasassun agwagi na da dadin ci, sun kuma sha bamban da saura. Ina sha'awarsu sosai.'
|