Ofishin jakadancin kasar Sin a Nijeriya da gwamnatin Nijeriya sun dauki matakai masu yakini wajen ceto ma'aikatan Sin biyar da aka yi garkuwa da su a jihar Rivers da ke kudu maso gabashin kasar Nijeriya, amma ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya ko wani mutum da ta amince da daukar alhakin wannan al'amari, wadannan ma'aikatan kasar Sin 5 ma an kasa gane inda suke.
A cikin irin wannan hali ne, a ran 7 ga wata da maraice, Malam Xu Jianguo, jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Nijeriya ya kai ziyara ga Olusegun Obasanjo, shugaban kasar Nijeriya a fadar shugaban kasar, inda ya gabatar masa da damuwa da shugabannin kasar Sin ke nunawa ga al'amarin ma'aikatan Sin da aka yi garkuwa da su, inda suka tattauna kan yadda za a cece su. Malam Li Le, sakataren jakadan kasar Sin a Nijeriya ya bayyana cewa, shugaba Obasanjo yana mai da hankali sosai ga al'amarin nan. Ya ce, "shugaba Obasanjo ya nuna rashin jin dadi da al'amarin da ya auku, ya bayyana cewa, gwamnatin kasarsa ta fahimci babbar damuwar da shugabannin kasar Sin da gwamnatinta ke nunawa. Zai dauki alhakin daidaita al'amarin shi da kansa, ya hakkake, tabbas ne za a daidaita al'amari yadda ya kamata, kuma yana fatan al'amarin ba zai kawo cikas ga bunkasuwar dangantakar aminci ta hadin kai a tsakanin kasashen biyu kamar yadda ya kamata ba."
Kafin wannan, jakada Xu Jianguo ya riga ya gana da sakataren din din din na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Nijeriya da babban sifeton 'yan sanda na kasar, inda ya bayyana musu babbar damuwar da gwamnatin kasar Sin ke nunawa a kan lafiyar ma'aikatan da aka yi garkuwa da su, ya nemi bangaren Nijeriya da ya dauki tsaurarran matakai cikin sauri don tabbatar da kare lafiyar wadannan 'yan kasar Sin.
Yayin da kakakin watsa labaru na babbar hukumar 'yan sanda ta kasar Nijeriya ke karbar ziyarar da manema labaru suka yi masa, ya bayyana cewa, "irin wannan aiki da wadannan 'yan ta kife suka yi bai dace da manufar gwamnatin kasar Nijeriya ba. Gwamnatin ta ki yin haka, kuma za ta yi duk abubuwa da take iya yi bisa ikonta don kawo karshen aikace-aikace da ake yi na yin garkuwa da mutane a yankin Niger Delta. Gwamnatin ta riga ta tattauna a tsakaninta da wasu kungiyoyi masu zaman kansu da unguwoyin jama'a don neman hanyar da za a bi wajen daidaita irin wannan matsala."
A ran 6 ga wata da yamma, Malam Wang Lei, babban mashawarci na ofishin jakadanci na kasar Sin a Nijeriya ya shugabanci wata kungiyar ba da agaji da ke kushe da ma'aikatan ofishin jakadancin da na kamfanin wadannan ma'aikatan kasar Sin, zuwa jihar Rivers inda al'amarin ya auku, don ba da taimako da sanya ido kan mataki da 'yan sanda na Nijeriya za su dauka don ceton ma'aikatan nan.
Malam Yao Hengbin, mataimakin babban manajan reshen kamfanin CCECC na kasar Sin a kasar Nijeriya shi ma ya je jihar Rivers da ke kudu maso gabashin kasar. Ya bayyana cewa, "yanzu, hankalinmu a kwance yake, domin muna ganin cewa, irin wannan al'amari ba safai ya kan auku ba. Amma kamar yadda muke yi a kullum, wajibi ne, a sami 'yan sanda a duk wuraren aikinmu. Bayan aukuwar al'amarin, mu ma mun yi la'akari da inganta aikin tsaron kai, Wato, mu kara kokari wajen yin gadi a wuraren aikinmu da mazaunanmu. Kuma a ko wace rana, mu sanya ido a kan wurare da 'yan sanda ke gadi, ta yadda za mu kara wasu 'yan sanda a wasu wurare ya kamata."
Yanzu, ofishin jakadancin kasar Sin a Nijeriya ya riga ya sanar da al'amarin nan ga duk kamfanonin kasar Sin da ke a kasar, kuma ya neme su da su kara daukar matakan tsaro don kauce wa irin wannan al'amari ya sake aukuwa. (Halilu)
|