Yawancin mutanen kabilar Shui suna zama a gandumar Sandou ta kabilar Shui mai cin gashin kanta. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar Shui ya kai misalin dubu dari 4. Suna da yarensu, amma yanzu suna kuma amfani da harshen Sinanci a rayuwarsu ta yau da kullum.
A karshen karni na 19 da ya gabata, rukunonin kasashen mulkin mallaka sun kai hare-hare kan yankunan da mutanen kabilar Shui suke da zama. An kuma fara noman tabar wiwi, ba a iya noma hatsi ba a yankunansu. Sa'an nan kuma, a karkashin azzaluman masu arziki, manoma sun shiga hali mafi talauci. Mutanen kabilar suna cin bawon itatuwa, kuma suna yin amfani da bargon ciyawar shimkafa lokacin da suke barci.
Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an yi gyare-gyaren gurguzu a yankunan kabilar Shui ta hanyar dimokuradiyya kamar yadda aka yi a sauran yankunan duk kasar Sin. A shekarar 1957, an kafa gandumar Sandou ta kabilar Shui mai cin gashin kanta. Sakamakon haka, jama'ar kabilar Shui sun fara tafiyar da harkokinsu da kansu. A karkashin taimakawar gwamnatin kasar, an sare gonaki masu ban ruwa da yawa, yawan hatsin da aka samu ma ya yi ta samu karuwa. A da, babu masana'antun zamani a yankunan kabilar, amma yanzu an riga an kafa masana'antun hakar kwal da samar da wutar lantarki da kuma masana'antun sarrafa amfanin gona. An kuma horar da kwadagon kabilar Shui da yawa. A waje daya kuma, an raya zirga-zirga cikin sauri a yankunan da kabilar Shui take da zama. Bugu da kari kuma, an riga an shimfida hanyoyin mota da na dogo da na ruwa a yankunan da mutanen kabilar Shui suke da zama. Sa'an nan kuma, yanzu yawan yaran da suke karatu a cikin makarantun firamare ya kai kashi 80 cikin kashi dari ko fiye. Sakamakon haka, zaman rayuwar jama'ar kabilar Shui ya samu kyautatuwa sosai.
Mutanen kabilar Shui suna da hankali sosai. A cikin shekaru da yawa da suka wuce, sun yi tallafe-tallafe masu dimbin yawa. Sun fi kwarewar rera wakoki da yin raye-raye.
Mutanen kabilar Shui ko maza ko mata sun fi son sanya tufafi masu shudi da baki.
Bisa al'adar kabilar Shui, wani saurayi ya iya aurar mace daya. Yau da shekaru dari 2 ko 3 da suka wuce, samari da 'yan mata sun nemi soyayya da aure cikin 'yanci. Lokacin da wani saurayi da wata mace suke yin bikin aure, ango ba ya zuwa gidan amarya, sai abokansa ne suke zuwa domin dawo da amarya. Amarya ta je gidan ango da kafa. Bayan an shirya wa baki liyafa, a kashegari ko a wannan rana ne amarya ta koma gidan iyayenta ta kuma ci gaba da yin zama a gidan iyayenta har na tsawon rabin shekara. Sa'an nan kuma ta je gidan mijinta ta yi zama a gidan mijinta.
Mutanen kabilar Shui suna bin addinin nasu, kuma suna da bukukuwa iri iri nasu.(Sanusi Chen)
|