Wakilin Rediyon kasar Sin dake birnin Lagos ya ruwaito mana labari cewa , a ran 7 ga watan nan a birnin Abuja , hedkwatar kasar Nijeriya , Olusegun Obasanjo , Shugaban Kasar Nijeriya ya jaddada cewa , shi da kansa zai kula da aikin ceton Sinnawa 5 da aka yi garkuwa da su kwanan baya .
Mr. Obasanjo ya yi wannan bayani ne lokacin da yake ganawa da Xu Jianguo , Jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya . Ya Jaddada cewa , za a warware wannan matsala cikin lumana kuma ya yi fatan wannan lamarin ba zai kawo illa ga yalwatuwar huldar zumunci da hadin gwiwa tsakanin kasar Nijeriya da Sin ba.
Mr. Xu ya nuna godiya ga hukumomin da abin ya shafa na kasar Nijeriya saboda suke yin kokari don ceton sinawan 5 . Kuma ya bayyana cewa , Hu Jintao , shugaban kasar Sin da Wen Jiabao , firayin ministan kasar Sin da sauran shugabannin kasar Sin da gwamnatin kasar da jama'a suna mai da hankali kwarai da gaske kan wannan lamarin kuma suna fatan bangaren Nijeriya zai dauki matakai masu yakini don tabbatar da sakin wadannan sinawan cikin lumana .(Ado)
|