Wakilin rediyon kasar Sin dake birnin Lagos ya ruwaito mana labari cewa , a ran 7 ga watan nan wani jami'in da bai sanar da sunansa ba ya ce, shugaban wata karamar kabilar Emohua da ke jihar Rivers ta kasar Nijeriya ya bayyana cewa , zai ba da taimako ga ceton Sinnawa 5 da aka yi garkuwa da su kwanan baya , kuma ya amince da cewa , za a saki Sinawan cikin lafiya .
Wannan jami'in ya ce , shugaban ya bayyana cewa , zai yi amfani da matsayinsa don ba da taimako ga Kungiyar ceto ta musamman ta Ofishin Jakadancin Kasar Sin da gwamnatin Wurin da 'yan sanda don ceton sinawan 5 . Idan za a yi aikin ceton yadda ya kamata , to , nan gaba kadan za a saki wadannan sinawan .
Amma duk da haka wannan jami'in bai sanar da sunan shugaban karamar kabilar ba.(Ado)
|