Jiya kungiyar agaji ta musamman da ofishin jakadancin kasar Sin a Nijeriya ta kafa ta isa Harcourt, hedkwatar jihar Rivers, wato wurin da aka sace injiniyoyin kasar Sin biyar ke nan, don su daidaita ayyukan ceto tare da gwamnati da 'yan sanda na wurin.
A yayin da jakadan kasar Sin a Nijeriya Mr.Xu Jianguo ke yin hira tare da wakilinmu a ran nan, ya ce, ofishin jakadancin kasar Sin yana mai da hankali sosai a kan al'amarin, kuma yana tuntubar manyan jami'an Nijeriya, don isar musu kulawar gwamnatin kasar Sin da shugabanninta.
Ban da wannan, zaunannen sakataren ma'aikatar harkokin waje ta Nijeriya, Mr.Hakeem Baba-Ahmed ya ce, shugaban kasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo yana kulawa da al'amarin sosai, kuma ya ba da umurni na musamman ga sassan da abin ya shafa don su gudanar da ayyukan ceto nan da nan. Bangaren Nijeriya zai yi iyakacin kokarin aiwatar da ayyukan ceto.(Lubabatu)
|