Kasar Sin tana nuna kulawa sosai a kan sace wasu injiniyoyinta da aka yi a Nijeriya, kuma a yanzu haka tana kokarin neman kubutar da su.
A ran 5 ga wata, wasu dakaru sun sace injiniyoyin kasar Sin biyar a jihar Rivers ta kasar Nijeriya.
A jiya ranar 6 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Liu Jianchao ya ce, shugabannin kasar Sin suna nuna kulawa sosai a kan al'amarin. Shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao da firaministan kasar, Mr.Wen Jiabao sun nemi ma'aikatar harkokin waje ta kasar da kuma ofishin jakadancinta a Nijeriya da su yi iyakacin kokarin tabbatar da zaman lafiyar wadanda aka sace da kuma kubutar da su. Bayan haka, jiya da dare, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin shi ma ya bayyana cewa, ma'aikatar ta riga ta fara aiki da shirin gaggawa, don gudanar da ayyukan ceto.
A wata sabuwa kuma, an ce, jiya ofishin jakadancin kasar Sin a Nijeriya ya kafa kungiyar agaji ta musamman, kuma kungiyar ta tashi zuwa hedkwatar jihar Rivers, don daidaita ayyukan ceto tare da gwamnati da 'yan sanda na wurin. Har zuwa yanzu, babu kungiyar dakaru da suka yi shelar daukar alhakin al'amarin.(Lubabatu)
|