Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-06 16:41:00    
Shugabannin kasar Sin sun lura da Sinawa da aka sace su a kasar Nijeriya sosai

cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Liu Jianchao ya yi bayani a ran 6 ga wata, cewa a ran 5 ga wata, 'yan bindiga sun yi awon gaba da Sinawa biyar masu aikin injiniya a jihar Rivers ta kasar Nijeriya. Shugabannin kasar Sin sun mai da hankali sosai kan batun. Shugaban kasar Sin Hu Jintao da firayim ministan kasar Wen Jiabao sun bukaci ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da kuma ofishin jakadancin Sin da ke Nijeriya da su nemi dabaru don tabbatar da lafiyar wadannan sinawa biyar, da kuma yin iyakacin kokarinsu wajen cetonsu.

Yanzu hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin suna hadin kai tare da hukumomin da abin ya shafa na kasar Nijeriya cikin yakini domin ceton Sinawa da aka yi garkuwa da su. Haka kuma hukumomin kasar Nijeriya sun riga sun fara bincike kan batun. Amma ya zuwa yanzu babu wata kungiyar dakaru da ta dauki nauyin sace wadannan Sinawa.(Kande Gao)