Rahotanni da dumiduminsu daga ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya sun tabbatar mana da cewar da safiyar ranar juma'annanne a jihar Rivers dake kudancin Nijeriya wasu yan bindiga suka yi awon gaba da wasu Sinawa.
Wang Lei, Jami'i mai kula da harkokin siyasa na ofishin jakadancin kasar Sin dake Abuja, fadar gwamnatin tarayyar Nijeriya, ya shaida wa kamafanin dillancin labarun xinhua ta waya cewar da misalin karfe biyar na asubahin yau juma'a ne aka yi awaon gaba da wadannan sinawa biyar a wani wuri da ake kira Emohua na Jihar Rivers.
Jami'in ya cigaba da cewar yan bbindigan kuma sun wawushe kayayyai masu dimbin yawa da suka kai na kudi dalar murkla dubbai daga hannun Sinawan, kayayyakin sun hada da wayoyin salula da dai sauransu.
A halin da ake ciki dai a cewar Jami'in, ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya na iya kokarinsa domin ceto wadannan sinawan, sannan kuma ofishin jakadancin na tuntubar karamar hukumar ta Emohua da kuma gwamnatin jihar ta Rivers.
Har ya zuwa yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki nauyin sace sinawan. ( ilelah)
|