Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-05 12:51:21    
Sabuwar babbar daraktar kungiyar WHO ta fito a gaban jama'a a karo na farko

cri

An labarta, cewa Madam Margatet Chan, sabuwar babbar daraktar kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta fito a gaban jama' a karo na farko jiya Alhamis a birnin Geneva, inda ta burge mutane kwarai da gaske.

A wannan rana da maraice, Madam Margaret Chan ta shirya taron watsa labrai na farko a dakin taro dake karkashin dogayen benaye na WHO, inda 'yan jarida suka nuna sha'awa sosai ga sauraron jawabin da ta yi. Da farko dai, Madam Margaret Chan ta gaida 'yan jaridan a albarkacin sabuwar shekara; Daga baya dai ,ta yi gajeren jawabi game da muhimman ayyuka guda biyu da za ta yi a wannan shekara, wato maganar Afrika da kuma maganar mata. Bayan haka, sai ta amsa tambayoyin da maneman labaru suka yi mata.

Nan take, 'yan jaridan suka mai da hankulansu sosai kan manyan manufofi guda biyu da kungiyar kiwon lafiya ta duniya wato WHO za ta aiwatar da su nan da 'yan shekaru masu zuwa. Tambayoyin da 'yan jaridan suka yi sun hada da magana kan yadda za a tabbatar da makasudin kungiyar kiwon lafiya ta duniya, da hakikanan matakai da za a dauka don kyautata halin da Nahiayr Afrika take ciki a halin yanzu da kuma magana kan yadda za a samo makudan kudade da za a ware don hana yaduwar miyagun cututtuka masu yaduwa da dai sauransu. Madam margaret Chan ta yi nuni da, cewa lallai aikin kyautata yanayin tsabta na jama'a na kasashen Afrika na dogaro da bunkasuwar tarttalin arizikin wadannan kasashe daga dukkan fannoni. ' Sai dai an samu ci gaban tattalin arziki ne za a iya samun karin kudade wajen yin aikin jiyya da kuma shawo kan cututtuka iri daban daban masu yaduwa. A sa' i daya kuma Madam Margaret Chan ta yi na'am da, cewa har ila yau dai cututtuka masu yaduwa sun kasance tamkar kalubale ne mafi girma dake gaban aikin kiwon lafiya na jama'a. Sa'annan ta bada misalin cewa, akwai kananan yara 3,000 da suke mutuwa a kowace rana a duniya sakamakon ciwon zazzabin sauro ; Ban da wannan kuma, ciwon murar tsuntsaye na yin illa ga lafiyar bil dama. Daga baya Madam Margaret Chan ta yi kashedin, cewa wajibi ne a mai da hankali sosai kan wadancan cututtuka da ba a taba kamuwa da su ba a da domin kuwa lalacewar muhallin zama yakan haifar da sabbin cututtuka da za su yi illa ga mutane masu yawan biliyan 6 na duk duniya. Madam Margaret Chan ta jaddada, cewa a gaban wadannan kalubale, ya kamata dukkan kasashen duniya su dauki nauyin dake bisa wuyansu na kafa tsarin shawo kan annobar cututtuka da suke fama da su gwargwadon iyawa.

A gun ganawa da manema labaru, Madam Margaret Chan ta tabo magana kan aikin da kungiyar kiwon lafiya ta duniya wato WHO zata yi, inda ta furta cewa, dole ne a yi namijin kokari wajen aiki. Yanzu, ana kwaskwarimar hukumomin kungiyar WHO lami-lafiya. Yayin da wassu 'yan jarida suka yi tambaya kan maganar neman shiga cikin kungiyar WHO da hukumar Taiwan take yi, sai Madam Magaret Chan ta jaddada, cewa ka'idar kasar Sin daya tak ta rigaya ta samu amincewa daga akasarin kasashe mambobin wannan kungiya. 'A matsayin wata babbar daraktar kungiyar', in ji ta, ' ko shakka batu za ta ci gaba da bin wannan ka'ida'. A sa'i daya kuma ta fadi cewa kungiyar WHO tana kula da zaman alhari da kuma lafiyar jikin jama'ar Taiwan. Dimbin kwararru na yankin Taiwan za su samu damar halartar tarurruka da kuma harkoki da kungiyar Who za ta shirya.

'Yan jarida sun gano cewa, Madam Margaret Chan ta amsa tambayoyi 17 da aka yi mata a gun ganawa da manema labaru, wato ke nan ba ta ki amsa tambaya ko daya ba. Lallai ta burge mutane kwarai da gaske. ( Sani Wang )