Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-04 21:12:33    
Bayanin Gwamnatin kasar Sin kan zaman rayuwar mata da yara (Kashi na uku)

cri

Ofishin labaru na Majalisar Gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da labari cewa , gwamnatin kasar Sin ta riga ta tsai da manyan makasudai 9 da za a tabbatar da su zuwa shekarar 2020 , ciki har da raya aikin mata da yara da kyautata tsarin dokokin shari'a da rage bambamcin dake tsakanin birane da kauyuka kuma tsakanin shiyyoyi daban daban . A cikin shirinmu na yau za mu yi 'dan bayani kan kyautata zaman rayuwar mata da yara .Me ya sa yanzu kasar Sin ta gabatar da maganar raya zaman al'umma mai jituwa ? Me Ya sa aka mai da wannan magana bisa matsayin wata sanarwa na tsarin ka'ida? To , bari mu tabo magana kan wadannan matsalolin .

Tun daga shekarar 1978 zuwa yanzu , an riga an shafe shekaru 28 ana yin gyare-gyaren tattalin arzikin kasar Sin , kuma an samu manyan nasarorin da suka jawo hankulan kasashen duniya ko a wajen karuwar tattalin arziki ko kuwa a wajen sauyawar tsarinsa. Kasar Sin kasa ce mai tasowa wadda take da mafi yawan mutane a duniya . Yawan mata ya kai kimanin kashi 50 cikin 100 . Karfafa zaman daidaici da aikin mata ba kawai yana da muhimmanci ga yalwatuwar kasar Sin ba , har ma zai kawo tasirin musamman ga ci gaban 'dan Adam a duniya .

Kasar Sin za ta kara karfin kiyaye ikon mata da yara . A ran 16 ga watan Janairu , wani jami'in Kungiyar kiyaye ikon mata da yara ta kasar Sin ya bayyana cewa , a wannan shekara kasar Sin za ta ci gaba da karfafa aikin wannan fanni wato za ta kara karfin kiyaye ikon mata da yara .

A Unguwar Haidian na birnin Beijing akwai wata makarantar musamman wadda take karbi yara masu karacin basira wato Makarantar firamare ta Peizhi . Wakilin Rediyon kasar Sin ya kai ziyara a wannan makarantar , inda ya gano cewa , a wannan makarantar akwai cikakkun kayayyakin koyarwa da isassun malamai masu koyarwa . Koyon ilmi da zaman yau da kullum na yaran ba su da bambanci bisa na daidaitattun yara . Liu Xuting , yaro mai karancin basira ya gaya wa wakilinmu cewa , yana jin dadi sosai a cikin makarantar .

Ya ce , kawunai da goggo masu yawa suna kula da ni . A nan ina farin ciki a kowace rana . A wajen koyon ilmi , malamai maza da mata suna kula da ni . Zan mai da hankali sosai kan karatu .A nan kasar Sin an kara mai da hankali kan tarbiyyar nakasassun yara kuma ana lura da su fiye da da . Wannan ya bayyana cewa , aikin da kasar Sin ta yi a wajen kiyaye ikon mata da yara ya kara karfi sosai . A cikin 'yan shekarun da suka shige , a nan kasar Sin daga shugabanni zuwa mutanen farar hula sun mai da muhimmanci kan kiyaye iko da moriyar yara da mara wadanda suke matsayi maras karfi . A gun taron aikin da Kungiyar kiyaye ikon mata da yara ta kasar Sin ta shirya a ran 16 ga watan Janairu a nan birnin Beijing , wakilinmu ya sami labarin cewa , wannan aikin ya sami ci gaba kwarai da gaske a cikin watan Nuwamba na shekarar 2006 da ya wuce ba da dadewa ba . (za a cigaba)