Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-03 20:20:09    
Amsoshin tambayoyinku

cri

Kwanan baya, mun sami wasiku da yawa daga wajen masu sauraronmu, inda suka sanar mu da ra'ayoyinsu a kan shirye-shiryenmu, sun kuma ba mu shawarwari masu kyau.

A cikin wasikar da Jekadafari Youth Radio Listener's Association da ke jihar Gombe, Nijeriya, ta turo mana, ya ba mu wasu shawarwarinsu, sun ce, batun shirye-shiryenku na safe, akwai matsala sosai ta wajen rashin karfi da kuma rashin kama ku a kai a kai. Game da shirye-shiryenku, ya kamata ku aika wa ko wane mai sauraronku jadawalin shirye-shiryenku sabbi. Game da ambulan din da kuke aikawa masu sauraronku da kuka ce kun biya kudin kan sarki, hakika mu a nan yankinmu, wato jihar Gombe, har yanzu ma'aikatar sakonni ba su amince da wannan ambulan din ba, don haka, ku sake tuntubansu. Mun gode da wadannan sahihan shawarwarin da Jekadafari Youth Radio Listener's Association ta ba mu, da kuma matsalolin da suka sanar da mu, gaskiya shawarwarinku na da amfani kwarai a wajen kyautata aikinmu, mun gode, kuma a yanzu haka, mun sanar da sassan da abin ya shafa a kan matsalolin, kuma game da batun kan sarki, duk kasar da ke cikin kungiyar rarraba wasiku ta duniya ta amince da ambulan da muka aiko muku, amma muna kokarin neman daidaita wannan matsala, tare da fatan Allah ya taimaka mana.

Akwai kuma malam Musa Tijjani daga jihar Kano, tarayyar Nijeriya, wanda ya rubuto mana cewa, mun gode da irin wannan gasa da kuka shirya mana game da Panda, shin zan iya amsa tambayarku ta hanyar Email? Ko sai ta Box? Bayan haka, a cikin sakon da malam Sanusi Isah Dankaba daga birnin Keffi, jihar Nassarawa ta Nijeriya ya aiko mana, ya ce, don Allah, a ina ne kuka sa gasarku ta kacici-kacici a shafinku na internet? To, yanzu mun fara sabuwar gasarmu ta kacici-kacici dangane da garin Panda, kuma masu sauraronmu kuna iya amsa tambayoyinmu ta hanyar Email ko kuma ta Box duka, wato yadda kuka ga dama ke nan. Sa'an nan, muna sa gasar a farkon kan shafinmu na internet, da ku bude, za ku gani a sama, muna kuma fatan masu sauraronmu za ku yi kokarin shiga gasar.

Sai kuma sako daga Abdu Bello Rishi, mai maganin gargajiya, Yankali Jos na nuni da cewa, ina jin dadin shirye-shiryenku, sai dai da kyar na samu yadda zan aiko da sakon nawa, don haka ku yi wa hanyar aiko muku da sako folder mai zaman kanshi. Malam Abdu Bello, mun gode da wannan shawararka. Yanzu muna duban shawarar. Amma kafin mu sami wani sakamako dangane da shawarar, kai da kuma sauran masu sauraronmu, kuna iya aiko mana da sakonninku zuwa akwatin gidan wayarmu a kasar Nijeriya, wato Lagos Bureau, China Radio International P.O.Box 7210, Victoria Island, Lagos Nijeriya. Ko kuma ku aiko mana wasiku zuwa nan kasar Sin, wato, Hausa Service CRI-24, China Radio International, P.O.Box 4216, Beijing, P.R.China,100040. kuna kuma iya aiko mana Email a kan Hausa @cri.com.cn.

Sai kuma malam Salisu Muhammad Dawanau, mazauni Garki, Abuja na tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "da fatan kuna lafiya kamar yadda nake a nan Abuja, Nijeriya, ina fatan ayyuka suna tafiya daidai-wa-daida kamar yadda kuke bukata. Wannan wasika ta gaisuwar sada zumunci ne a gare ku baki daya. Da kuma yin tsokaci, kamar yadda na saba, dangane da shirye-shiryenku na rediyo da na shafinku na Internet. Kamar yadda kowa ya sani, rediyo wata kafa ce ta samun labarai cikin hanzari kuma kai tsaye, to, a gaskiya, mu kan yaba muku wajen yada labarai na kasar Sin da kuma na nahiyar Asiya cikin hanzari ba tare da kun gurbata labaran ba kamar yadda kafofin yada labarai na kasashen yammaci da na Turai kan yi. Hakika, wannan abin yabo na sahihi. Shafinku na 'internet' kuwa ya zama tamkar hanyar samun bayanai masu inganci da kuma armashi, na tabbata yawa-yawan masu saurarenku ta wannan hanya suna gamsuwa da irin bayanan da su kan samu ko su kan tattara don karin ilmi da kuma fahimtar abin da kan faru a kasar Sin da kuma nahiyar Asiya baki dayanta. Ina fatan za ku dada zage damtse, da kuma yin himma wajen ganin kun dada kyautata shirye-shiryenku na yau da kullum, kun san an ce, idan kana da kyau, to ka kara da wanka." Malam Salisu Dawanau tsohon mai sauraronmu ne, wanda ke sauraron shirye-shiryenmu a kullum, kuma ke dinga ba mu ra'ayoyinsa da shawarwarinsa, gaskiya ya ba mu goyon baya kwarai, dukan ma'aikatan sashen Hausa na rediyon kasar Sin muna godiya kwarai da gaske gare shi. Ban da wannan, muna kuma kira ga sauran masu sauraronmu, sai ku dinga sauraron shirye-shiryenmu, ku samu bayanai daga shafinmu na internet, sa'an nan ku ba mu ra'ayoyinku, don mu kara kyautata su. Da fatan Allah ya bar zumunci a tsakaninmu.