Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-03 20:17:14    
Wani mutum na zamanin da na kasar Sin mai suna Zheng Banqiao

cri

Zane-zanen kasar Sin suna da halayensu na musamman na kansu kawai a rukunonin fasahohi na duniya. Zheng Banqiao shi ne mashahurin mai yin zane-zane na kasar Sin na karni na 18 .

Daga cikin masu yin zane-zanen gargajiya kan gora na kasar Sin, idan ka tambaye mu cewa, wane ne mai yin zane-zane kan gora da ya fi kyau, to ba shakka za a amsa maka cewa, shi ne Zheng Banqiao . An haifi Zheng Banqiao a shekarar 1693 a wani gidan malaman koyarwa da ke lardin Jiangsu na kasar Sin, tun lokacin da yake karami, mahaifiyarsa ta mutu, gidansu ya yi fama da talauci sosai. Sunansa da aka rada masa tun lokacin da aka haife shi shi ne Zheng Xie, , amma sa'anan kuma ana kiansa da cewar wai Zheng Banqiao duk bisa sakamakon da ya sa sunansa kan zane-zanen da ya yi cewar wai Zhengxie na Banqiao, Amma shi kansa yana kiransa da cewar wai Ban Qiao shi ne saboda gidansu na da wata bukka da ke da dakunan kwana biyu kawai a bakin kogin kiyaye gundumar da yake zama., a kan kogin, an kafa wata gadar katako mai sauki, wato Ban Qiao cikin Sinanci ke nan, saboda haka masu yin zane-zane suna kiran wannan gadar katako da cewar Ban Qiao don yin tunawa.

An bayyana cewa, kafin shekarunsa su kai 40 da haihuwa, Zheng Banqiao shi ne wani mai karatu da bai yi suna sosai a duniya ba, tamkar yadda yawancin masu fasahohi wato bokaye suka yi, ya ci hasara sau da yawa wajen jarrabawar da aka yi don samun mukami. Ya zuwa shekarunsa na haihuwa da suka kai 43, Zhen Banqiao ya sami wani mukami, daga nan sai ya hau kan kujerun mukaminsa a wasu gundumomi.

Zhen Banqiao ya hau kan kujerar mukaminsa har cikin shekaru 12, ya ki cin hanci da rashawa sosai tare da yin aikin bajinta sosai wajen kula da harkokin hukuma, shi ya sa a zamaninsa, ba wanda ke cikin gidan kurkuku. A lokacin da aka sha fama da bala'in halitta, Zheng Banqiao bai boye kome ba sai bayar da rahoton gaskiya kawai ga gwamnati don yin iyakacin kokarin ba da rokonsa ga gwamnati don fitar da jama'ar farar hula daga mawuyacin hali da samar musu taimako. Sa'anan kuma ya ba da umurni ga masu sukuni da su samar da abinci ga wadanda ke fama da talauci da bala'I, har ma shi kansa ya bayar da albashinsa kyauta. A lokacin da aka gamu da bala'I mai tsanani sosai, sai ya tsai da kuduri ba tare da shakkar kowa ba ya bude wa jama'ar farar hula siton ajiye hatsi na gwamnati don magance mawuyacin halin da suke ciki, mabiyansa dukansu sun shawo kansa da cewa, ya kamata ya yi aikin nan bayan da aka yi masa yarda, amma ya bayyana cewa, in na jiran iznin da za a gabatar mini, to jama'ar farar hula za su mutu ba shakka, ni kaina zan dauki nauyin nan bisa wuyana, ta hakan, Zheng Banqio ya ceci mutane da yawa, amma shugabansa ya yi fushi sosai bisa sakamakon aikinsa na ceton mutane ba tare da samun izni ba, a karshe dai Zheng Banqiao ya yi fushi kuma ya yi murabus daga mukaminsa, sa'anan kuma ya yi zama a cibiyar al'adu ta birnin Yangzhou na kasar Sin na wancan zamani.

Daga nan, Zheng Banqiao yana ciyar da iyalansa ta hanyar sayar da zane-zanen da ya yi. A duk zaman rayuwarsa, ya yi zane-zane dangane da wani irin fure da ake cewa "Orchid" (cikin Turanci) da gora da duwatsu kawai. Zane-zanensa na da daraja sosai a halin yanzu. Ban da zane-zanen da ya yi, ya kuma kware sosai wajen yin rubuce-rubuce tare da tsara wakoki, rubuce-rubucensa na da halayen musamman sosai, kuma wakokinsa har yau ana yada su a tsakanin jama'a. Musamman ma a cikin wakokinsa, ya bayyana wahalolin da manoma suke sha da mawuyacin hali da suke ciki, wadannan sun bayyana tausayi da ya yi wa jama'ar farar hula, shi ya sa suna da darajar abubuwan tarihi sosai. Har wa yau dai ana yada wani littafin da ke kunshe da dukan bayyanan da ya rubuta.(Halima)