Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-02 18:47:08    
Dakunan shan shayi na Beijing

cri

Al'adun shayi wani muhimmin bangare ne na al'adun kasar Sin mai dogo tarihi. Jama'a masu sauraro, yau za mu kai ziyara ga sharaharrun dakunan shan shayi 2 masu halin musamman, inda za mu fahimci al'adun shayi na kasar Sin.Ma'anar wannan jimla ita ce bakinmu masu girmamawa za ku kawo dakin shan shayinmu haske. Sabis masu sa tufafi irin na gargajiya na kasar Sin su kan fadi haka ne da yaren Beijing a lokacin da sansannen dakin shan shayi na Laoshe ya yi bako. Ko a yanzu, mutane su kan gano wasu halayen musamman na dakunan shan shayi na Beijing na zamanin da a cikin dakin shan shayi na Laoshe.

Mutanen Beijing sun fi son shan shayi irin na furen Jasmine. Saboda an kyafe danyun ganyayen shayi da furannin Jasmine, shi ya sa launin wannan shayi na da kore sosai, kuma cike yake da kamshi sosai. A cikin dakin shan shayi na Laoshe, ban da shayi irin na Jasmine, a kan samar da wani irin shayi na musamman. Bayan da aka cika kwaf da ruwa mai zafi, shayi da furanni sun bude sannu a hankali. Madam Yu Jing, mai kula da wannan dakin shan shayi ta yi karin haske cewa, 'A galibi dai, a kan hada kananan tohon shayi fiye da 160 da zare siriri, an kuma ajiye danyun furanni iri daban daban tare da wadannan tohon shayi, shan ruwan shayin tare da irin wadannan furanni kamar su jasmine da Camellia da osmanthus masu kamshi na zaki da kuma lily a cikin dogon lokaci yana amfanawa lafiyar mutane, musamman ma ga mata, ko kusa dukan danyun furanni na da amfani wajen kwaskwarimar kyan gani da fatan mata.'

Ban da shan shayi, mutane na iya kallon wasannin kwaiwakyo na gargajiya iri daban daban na kasar Sin a nan. A kan nuna wasannin kwaikwayo masu ban sha'awa a ko wace rana, kamar su wasannin wake-wake na Beijing Opera da acrobatics da wasan Kungfu na kasar Sin da dai sauransu. A lokacin da suke kallon wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin, kada mutane su manta da jin dadin ganin fasahar sabis a nan. Ba kamar yadda sabis suke a cikin sauran dakunan shan shayi ba, sabis na dakin shan shayi na Laoshe su kan yi amfani da wata tukunyar da ke da baki mai tsayin misalin mita 1 don cika kwaf da ruwa mai zafi. Sabis suna yin wasa da irin wannan tukunya sosai da sosai, ruwa mai zafi da ke cikin tukunya bai fita waje ba ko kadan. Yin amfani da irin wannan tukunya ya amfana wajen sanyaya ruwa mai zafi da ya fi dace da yin shayi.

Bugu da kari kuma, dakin shan shayi na Laoshe dakin shan shayi ne kawai da yake samar da shayi mai araha a cikin babban kwano a nan Beijing a yanzu. An ce, Ying Shengxi wanda ya kafa dakin shan shayi na Laoshe ya dasa harsashin sha'aninsa daga wajen sayar da irin wannan shayi mai araha, shi ya sa ko da yake bai ci riba ba, amma har zuwa yanzu dakin shan shayi na Laoshe na ci gaba da sayar da shayi mai araha a cikin babban kwano don tuna wa mutane kada su manta da tarihi. Darajar wannan shayi ta yi daidai da ta da, wato kudin Sin kwabo 2 kawai.

To, yanzu za mu jagorance ku wajen ziyarar dakin nuna fasahar shayi na sabon salo dan gaye da ke nan Beijing, sunansa Wu Fu An sami kwanciyar hankali a cikin dakin nuna fasahar shayi na Wu Fu., inda aka shimfida duwatsu masu launin kore shar a kasa, goldfish na iyo a cikin kananan tabkuna. An ajiye wasu kayayyakin gida na gargajiya masu daraja a nan. An kuma nuna kayayyaki masu daraja da ke da nasaba da shayi, a ciki kuma dubban tukwanen shayi masu kyan gani da aka yi da Purple Stoneware sun fi jawo hankulan mutane. Wadannan tukwane na ba da haske saboda an dade ana yin amfani da su don yin shayi.

Fasahar shayi ta kasar Sin ta fi mai da hankali kan ruwa da ganyayen shayi da kuma kayayyakin shayi da kuma fasahar yin shayi. Masu fasahar shayi na dakin nuna fasahar shayi na Wu Fu su kan yi wa mutane bayani kan ilmomi iri daban daban da suka shafi shayi. Mutane su kan ji dadin shan ingantattun ganyayen shayi saboda gabatarwar da masu fasahar shayi suka yi musu.

Mutanen Sin su kan mai da hankulansu kan abubuwa da yawa a fannin fasahar shayi, masu yawon shakatawa sun iya jin wadannan labaru daga bakin masu fasahar shayi. Ko da yake mutane sun yi amfani da shayi iri daya, amma su kan yi shayi masu dandano iri daban daban saboda halayen mutane sun sha bamban, haka kuma, wani mutum ya kan yi shayi masu dandani iri daban daban a lokuta daban daban. Yin shayi ya bukaci mutane da su fahimci fasahar shayi a zukatansu, sa'an nan kuma, yana bukatar hikimomin mutane. A ganin mutanen kasar Sin da yawa, yin shayi da kuma shan shayi sun iya kyautata halayen mutane.