Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-02 18:43:12    
Bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka tana kara samun sakamako mai kyau

cri

Daga ranar 17 zuwa ranar 24 ga watan Yuni na shekarar 2006, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao yake ziyarar aiki a kasashe 7 na Afirka wato Massar da Ghana da da Kongo(Brazaville) da Angola da Afrika ta kudu da Tanzania da kuma Uganda. Makasudin wannan ziyara shi ne zurfafa aminci da kara amincewa juna da habaka hadin kai da samun bunkasuwa tare. A gun ziyarar firayin minista Wen, an daddale wasu jarjejeniyoyi a jere, wadanda suka shafi siyasa da tattalin arziki da cinikayya da aikin likita da kimiyya da fasaha da dai sauransu. Wadannan yarjejeniyoyi suna amfana wa jama'ar Sin da kasashen Afirka, kuma za a kara kwarewar Afirka wajen samun bunkasuwa da kansu. Da aka tabo magana a kan ra'ayoyin gwamnatin kasar Sin a kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka da kuma hadin kansu, Mr Wen ya ce,

'Manufar da gwamnatin kasar Sin take tsayawa tsayin daka ita ce girmama wa juna da zaman daidai wa daida da moriyar juna da kada tsoma kabi a cikin harkokin gida na sauran kasashe. Mun yi imani cewa, jama'ar kasashe daban daban da yankuna daban suna da iko kuma suna da kwarewar warware matsalolinsu. Kasar Sin tana farin ciki sosai da ganin bunkasuwar tattalin arzikin Afirka da zaman jituwarsu da kara kyautattuwar dokoki da dimokuradiyya da zaman rayuwar jama'arsu mai kyau.'

Daga ranar 3 zuwa ranar 5 ga watan Nuwamba na shekarar 2006, kasar Sin shirya taron koli na dandalin tattaunawa a kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka da kuma taron ministoci na karo na uku a tsakaninsu. Babban taken wannan taro shi ne 'zumunci da zaman lafiya da hadin kai da samun bunkasuwa'. Shugabannin kasar Sin da na kasashe 48 na Afirka sun yi shawarwari bisa fuska fuska, a karshe dai, an bayar sanarwar Beijing, inda aka karfafa cewa, za su kafa sabuwar dangantakar abokantaka da ke tsakaninsu bisa manyan tsare tsare. Game da haka, shugaban kasar Massar Mohammed Hosni Mubarak ya bayyana cewa,

'A tsakake ne mu sanar da cewa, bangarorin Sin da Afirka mu yanke shawarar kafa sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare bisa tushen amincewa juna a kan siyasa da moriyar juna a kan tattalin arziki da koyon juna a kan al'adu.'

Dukkan kasar Sin da kasashen Afirka kasashe ne masu tasowa, sabo da haka suna fuskantar aiki daya wato warware matsalolinsu da samun bunkasuwar kansu a cikin lokacin bunkasuwar duniya bai daya. A yayin da kasar Sin take samun bunkasuwarta, tana mai da hankali da nuna goyon bayanta sosai ga kokarin da kasashen Afirka suka yi wajen samun bunkasuwa cikin dogon lokaci. An riga an rubuta wannan matsayin kasar Sin a cikin sanarwar Beijing. Game da haka, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayyana cewa,

'Kasar Sin tana nuna goyon baya ga kasashen Afirka da su karfafa karfinsu cikin hadin gwiwa da kuma warware matsalolin Afirka da kansu, kasar Sin kuma tana nuna goyon baya ga kokarin da kasashen Afirka suke yi wajen samun bunkasuwar tattalin arziki bai daya a shiyyarsu, haka kuma kasar Sin tana nuna goyon baya ga kasashen Afirka da su aiwatar da 'shirin sababbin abokai domin samun bunkasuwar Afirka'.'

Yanzu shekarar 2006 tana kusan karewa, amma dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta kara samun saurin bunkasuwa. A shekarar 2006, wato muhimmin lokacin da kasashen Sin da Afirka suka kafa dangantakar diplomasiyya cikin shekaru 50, bangarori biyu na Sin da Afirka sun dauki wasu manyan matakai domin kara sa kaimi ga dangantakarsu ta hadin kai da abokantaka da juna, kuma sun sami nasarori da yawa. Muna iya ganin cewa, shekarar 2006 ta riga ta zama wata muhimmiyar alama ga bunkasuwar dangantakarsu. Mun yi imani cewa, a cikin shekara mai zuwa wato shekarar 2007, dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka za ta kara samun babban ci gaba.

Jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na Sin da Afirka ke nan daga sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin daga nan birnin Beijing. Idan Allah ya kai mu, sai mako mai zuwa za mu kawo muku wani shirin musamman daban na Sin da Afirka domin taya murnar sabuwar shekara ta 2007. Danladi ya rubuta kuma ya farrasa wannan bayani, Shehu Illelah ya karanto muku a madadinsa. Jama'a masu sauraro, ku zama lafiya.(Danladi)