Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-01 20:46:32    
Takaitaccen bayani game da kabilar Uygur

cri

Mutanen kabilar Uygur suna kiran kansu Uygur. Ma'anar Uygur ita ce "gama kai" ko "hadin guiwa". Yawancin mutanen kabilar suna zama a yankunan da ke kudu da tsaunin Tianshan na jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar Uygur ya kai fiye da miliyan 8 da dubu dari 3. Suna kuma amfani da yaren Uygur. Suna da kalmomin yarensu.

Kabilar Uygur ta dade tana zama a duniya, kuma sun riga sun yi shekaru misalin dubu 2 suna yin mu'ammala da yankunan yammacin duniya da sauran yankunan kasar Sin.

A waje daya kuma, mutanen kabilar Uygur suna da al'adar yaki da masu hare-hare domin yin kokarin dinkuwar duk kasar Sin gaba daya.

Mutanen kabilar Uygur suna da al'adar aikin gona, musamman suna da fasahar noman auduga da 'ya'yan itatuwa. 'ya'yan itatuwa na jihar Xinjiang sun samu suna sosai a kasashen waje. Ana kuma kiran jihar Xinjiang garin 'ya'yan itatuwa.

Sa'an nan kuma kabilar Uygur tana da sana'ar hannu, inda suka kware kan dinkin kafet da silik da takalma da hannu.

A ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1955 ne aka kafa jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta.

A cikin shekaru fiye da 50 da suka wuce, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta samar wa jihar taimakon kudi da na kwadago da kuma kayayyaki iri iri. Ko da yake an sha wahalhalu da yawa, amma a karkashin kokarin kabilar Uygur da sauran kabilun da suke zama a jihar, an samu sauye-sauye sosai a jihar. Musamman yanzu, zaman rayuwar mutanen kabilar Uygur ya samu kyautatuwa sosai.

A da, mutanen kabilar Uygur da sauran kabilun da suke zama a jihar Xinjiang sun yi aikin gona da na kiwo kawai, babu masana'antun zamani. Amma yanzu, an riga an kafa masana'antun zamani iri iri, ciki har da masana'antun ingantaccen karfe da na kwal da na hakar man fetur da na samar da wutar lantarki da na kera motoci da na dukanci da dai makamatansu. Ana kuma shigi da ficin kayayyaki daga jihar zuwa kasashen waje.

Kabilar Uygur tana da dogon tarihi, tun da haka, tana da fasahar nune-nunen al'adunta ta musamman. An wallafi tatsuniyoyi da almara da Karin magana iri iri.

Bugu da kari kuma, mutanen kabilar Uygur suna jin alfahari sosai domin tana ilmin likitanci na musamman nata. Wannan ilmin likitancin kabilar Uygur yana daya daga cikin muhimman ilmomin likitanci na gargajiya na duk kasar Sin.

Mutanen kabilar Uygur ba su da babban gida, sai karamin gida. Bayan 'ya'yan suka yi aure, sai suna yin zaman kansu. Ana kuma girmama wa tsofaffi a al'ummar kabilar Uygur.

Mutanen kabilar Uygur sun fi son cin abincin da aka yi da garin alkama da shan madara da ti. Kuma suna bin addinin Musulunci. Sabo da haka, babbar sallah da karamar sallah muhimman bukukuwa ne na kabilar Uygur. (Sanusi Chen)