Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-29 17:49:42    
Takardar bayani daga gwamnatin kasar Sin kan ayyukan tsaron kasa a shekarar 2006

cri
Ran 29 ga wata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar da takardar bayani a kan ayyukan tsaron kasar a shekarar 2006, inda aka bayyana yadda kasar Sin ke aiwatar da ayyukan tsaron kasa da raya rundunar sojojinta ta zamani a fannoni daban daban. Kwararru suna ganin cewa, wannan takardar bayani ta bayyana cikakken imani da babbar niyya da kasar Sin ke nunawa wajen bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, ta nanata matsayi da kasar Sin ke tsayawa a kullum wajen aiwatar da manufar tsaron kasa irin ta tsaron kai, kuma ta nuna sahihin burin kasar Sin na yin kokari wajen kiyaye zaman lafiyar duniya da wadatuwa yadda ya kamata.

Wannan karo ne na biyar da kasar Sin ta bayar da irin wannan takardar bayani a kan ayyukan tsaron kasa tun bayan shekarar 1998. Abubuwa da ke cikin takardar bayanin sun hada da al'amuran zaman lafiyar kasar Sin, da manufofinta game da ayyukan tsaron kasa, da yawan kudi da take kashewa wajen gudanar da ayyukan tsaron kasa, da mayar da rundunar sojojinta da ta zama ta zamani, da hadin kai a tsakaninta da sauran kasashen duniya don kiyaye zaman lafiya da sauransu.

Takardar bayanin ta nuna cewa, kasar Sin ta ci gaba da inganta hadin kanta da manyan kasashe bisa halin da ake ciki, ta yi ta dankon aminci irin na makwabtaka a tsakaninta da kasashe da ke makwabtaka da ita, ta inganta ma'amala da take yi a tsakaninta da tarin kasashe masu tasowa daga fannoni daban daban, hulda da ke tsakanin bangarori biyu na mashigin teku na Taiwan ta sami bunkasuwa lami lafiya, a takaice, halin da kasar Sin ke ciki dangane da zaman lafiya yana da kyau. Sa'an nan kuma takardar bayanin ta yi bincike sosai a kan kalubale da kasar Sin ke fuskata wajen kiyaye zaman lafiyarta.

Da shehun malam Wen Bing, wanda ke aiki a cibiyar nazarin kimiyyar aikin soja ta kasar Sin ta tabo magana a kan wannan, sai ya ce, "ra'ayoyin nan sun bayyana kulawa da kasar Sin ke nunawa wajen kiyaye zaman lafiyarta da moriyar bunkasuwarta, yayin da barzana mai sarkakiya iri iri da gamayyar kasa da kasa ke fuskanta a fannin zaman lafiya, da saurin kara karfin kasar Sin a fannoni daban daban. "

Dangane da batun Taiwan, takardar bayanin ba ta kebe wasu shafunanta musamman don bayyana shi ba, ta yi bayani a kan wanan batu ne a cikin babinta na al'amuran zaman lafiya da manufofin tsaron kasa. Shehun malami Wen Bing ya ce, "na farko, ya kamata, sosai da sosai mu gane hadari da hali mai tsanani na neman "'yancin kan Taiwan "da 'yan a-ware ke yi a fannin doka; na biyu, ya kamata, mu gane abubuwa masu sarkakiya da kasar Amurka da sauransu suka yi a kan daidaituwar batun Taiwan. Na uku, takardar bayanin ya nuna babbar niyyarmu ta kiyaye dinkuwar kasar Sin gu daya da cikakken yankinta"

Takardar bayanin ta ce, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta yi ta inganta ma'amala da hadin kai a tsakaninta da sauran kasashe daban daban a fannin aikin soja. Shehun malami Wen Bing ya bayanna ra'ayinsa a kan wannan cewa, "irin wadannan abubuwa da aka bayyana a cikin takardar bayanin, sun alamanta cewa, rundunar sojojin kasar Sin tana son kara nuna amincewa a tsakaninta da rundunonin sojojin kasashe daban daban a fannin aikin soja da kuma inganta hadin guiwarsu don kare zaman lafiya. Su yi kafada da kafada da juna wajen sauke da nauyi da ke bisa wuyansu na kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya da duk duniya. "

Bayan haka, Shehun malami Wen Bing ya ce, takardar bayanin ta bayyana cikakken imani da babbar aniya da kasar Sin ke nunawa wajen bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, ta nanata matsayinta kan aiwatar da manufofin tsaron kasa irin na tsaron kai, kuma ta nuna sahihin burin kasar Sin na yin kokarin kiyaye zaman lafiya da wadatuwa a duk duniya. (Halilu)