Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-29 16:40:34    
Kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin suna inganta hadin kansu da manyan kamfanonin kasa da kasa

cri

A kwanakin baya ba da dadewa ba, a birnin Wenzhou na lardin Zhejiang da ke a kudu maso gabashin kasar Sin, kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin sun tattauna a tsakaninsu da wasu da ke cikin manyan kamfanonin kasa da kasa 500. Babban batu da suka tattauna a kai shi ne "samun damar zurfafa hadin kai tsakanin kamfanonin kasar Sin da na waje. Kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin wajen 100 da wakilan kamfanoni sama da 30 wadanda ke cikin manyan kamfanonin kasa da kasa 500 sun tattauna kan manufar hadin kansu da kuma makomarsu.

Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa a cikin shekaru 27 da suka wuce, kasar ta yi ta samun ci gaba da sauri wajen bunkasa harkokin tattalin arzikinta, matsakaiciyar jimlar kudi da take samu daga wajen samar da kayayyaki ya kan karu da kashi 9.6 cikin dari a ko wace shekara. Sakamakon haka, an samar da kyakkyawar dama ga manyan kamfanonin kasa da kasa da kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin don bunkasa harkokinsu. Malam Shi Guangsheng, shugaban kungiyar masama'antu da 'yan kasuwa na kasashen waje suka zuba masu jari ta kasar Sin ya bayyana cewa, "ya zuwa watan Satumba da ya wuce, kasashe da yankuna wadanda suka zuba jari a kasar Sin sun kai kimanin 200, yawan kudin jari da suka zuba a kasar ma ya wuce dalar Amurka biliyan 660. Yawan kudi da kasar Sin ke samu daga wajen kayayyaki da wadannan masana'antu ke fitarwa zuwa kasashen waje ya wuce rabin jimlar kudi da take samu daga cinikin waje. Ya zuwa karshen shekarar bara, yawan kudi da aka samu daga wajen kayayyaki da masana'antu masu zaman kansu ke samarwa ya kai rabin jimlar kudi da aka samu daga wajen kayayyaki da ake samarwa a kasar Sin wato GDP. A cikin shekarun nan biyar da suka wuce, wadannan masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin sun zuba kudi da yawansu ya karu da misalin kashi 30 cikin dari. "

An ruwaito cewa, a farkon lokacin da kasar Sin ta soma aiwatar da manufar gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa, yawancin masana'antu masu zaman kansu kanana da matsakaitan masana'antu ne, kuma suna fama da karancin kudi da fasaha. A wannan lokaci kuma ko da yake manyan kamfanonin kasa da kasa wadanda suka shiga kasar Sin ba da dadewa ba suna mallakar fasaha da kudin jari mai yawa, amma kasuwannin kasar Sin bakon abu ne gare su. Sabo da haka yayin da ake bunkasa tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri, ko shakka babu, masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin da manyan kamfanonin kasa da kasa sun hada kansu. Malam Tom Gorrie, mataimakin babban manaja na kamfanin Johnson&Johnson na kasar Amurka yana ganin cewa, "manyan kamfanonin kasa da kasa da kamfanonin masu zaman kansu na Sin sun sami kyakkyawar damar hadin guiwarsu, manyan kamfanonin kasa da kasa suna iya daure musu gindi a fannin kudi da fasaha, su taimake su wajen daga matsayinsu na gudanar da harkokinsu, da kyautata guraben ayyukansu. A wani hannu kuma, yayin da kamfanonin kasashen waje ke neman samun damar bunkasa harkokinsu, masana'antun za su ba su damar samun arziki, kamata ya yi, mu saba da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, mu hada kanmu da masana'antun sosai. "

Tun can lokaci, Kamfanin Coca Cola ya fara hadin kansa da masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin. Da Malam Cheng Jiwei, babban direktan reshen Sin na kamfanin Coca Cola ya tabo magana a kan hadin kan, sai ya ce, "ko ba dade ko ba jima, masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin za su zama masana'antun yin gwangwanin abun sha bisa matsayi na farko a duniya, ta hanya da muke bi wajen ba su fasaha, kuma bisa goyon bayan kamfanin Coca Cola, wadannan masana'antun kasar Sin za su bunkasa harkokinsu bisa matsayinsu mai rinjaye, su zama masana'antu masu kasaita a kasar Sin."(Halilu)