Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-29 16:26:10    
Labarai game da wasannin Olympic

cri

Aminai makaunatai, ko kuna sane da, cewa ayyukan wasanni na biyu na taron wasannin motsa jiki na Olympic na can can zamanin da, shi ne yin kokawa, wanda ya fi shere mutanen Girka ta zamanin can can da, wanda kuma ya zama sashen ilmi na dole ga dimbin makarantun Girka a wancan lokaci. A gun taro na 18 na wasannin motsa jiki na Olympic na can can zamanin da da aka gudanar a shekara ta 708 kafin haihuwar Annabo Isa Alaihisalam, aka mayar da wasan kokawa a matsayin daya dake cikin wasanni iri biyar.

Abu mai sha'awa, shi ne a wancan lokaci, akan yi wasan kokawa ne ba bisa matakin nauyin jikin 'yan wasa ba, wato ke nan akan zabi 'yan wasa abokan karawa ne ta hanyar kada kuri'a. An kuma tanadi, cewa a gun gasar, idan kafada da gwiwa da kuma kirji na dan wasa sun taba kasa, to kuwa sai ya rasa maki daya ; Idan ya rasa maki uku, to za a hukunta masa a kan cewa ai ya sha kaye ke nan ; Wadanda suka samu nasara a matakin farko, za su ci gaba da yin gasa cikin kungiya-kungiya ta hanyar kada kuri'a ; Duk wanda ya yi saura a gun gasar , shi ne mai cin nasara.

Mun san cewa, wasannin motsa jiki na zamanin yau sun yalwatu har sun kasance tamkar wata sura dake bayyana halin ingantuwar jikunan bil-adama da kuma gwada matsayin wayin kai na dan adam. Amma, a cikin gasanni Olympic na can can zamanin da ba haka ake ba, wato wassu 'yan wasa sukan yi kokawa cikin halin zubar da jini har da sadaukar da rayukansu a gun wassu ayyukan wasa domin samun daukaka. Wasan dambe dai ya bayyana haka a cikin gasannin Olympic na can can zamanin da.

Wannan wasan dambe yana kan muhimmin matsayi a cikin zamantakewar al'ummar tsohuwar kasar Girka. An dora wannan wasa cikin jerin gasanni na taron wasanni na 23 na Olympic na can can zamanin da da aka yi a shekara ta 688 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisalam.

Ka'idoji kan wasan dambe na taron wasannin Olympic na tsohuwar kasar Girka sun sha bamban da na zamanin yau, wato babu filayen musamman na gasanni a wancan zamani, kuma ba a kayyade yawan lokutan gasa da rarraba 'yan wasa bisa matakin nauyin jikinsu ba; Kazalika, akan tsaida 'yan wasa abokan karawa ta hanyar kada kuri'a kamar yadda aka yi a fannin gasar wasan kokawa.

Samun lambawan a gun taron wasannin Olympic na can can zamanin da, buri ne daya tak na dukkan 'yan wasa. Kuma wadanda suka samu lambawan sukan samu maraba irin ta jarumtaka bayan da suka koma garinsu. Wannan dai muhimmin dalili ne da ya sa 'yan wasa na tsohuwar Girka suka yi fintinkau wajen samun lambawan ko da suka sadaukar da ransu.

'Yan wasa da suka ci nasara a gun gasanni iri daban daban na taron wasannin Olympic sukan samu girmamawa sosai daga mutanen duk kasar Girka. Lambar zakara ba ma kawai ta kawo daukaka mai girma ga 'yan wasa da suka ci nasara ba, har ma ga iyalinsu da kuma garinsu. A cikin zukatan mutanen Girka, duk wadanda suka ci nasara a gun gasannin Olympic, su jarumai ne da gunki ya fi kaunarsu, kuma su 'yan kasa ne mafi nagarta na duk kasar Girka. A tsohuwar Girka, akwai wassu kalmomi kamar su wasan motsa jiki, da gasa da kuma yaki, a zahiri dai, kalma daya ne wato zakara. Don haka, mutanen tsohuwar Girka sukan nuna halin jarumtaka wajen shiga gasa domin zama zakara kamar yadda suka yi a wajen yaki.

A gun taron wasannin Olympic na can can zamanin da, akan zabi lambawan kawai, wanda akan sa wata zakarar reshen zaitun a kansa. Lallai ba a manta ba, a gun taron wasannin Olympic na Aden a shekarar 2004, mutane na ganin, cewa an sa wata zakarar reshen zaitun a kan kowane dan wasa yayin da yake hau kan dakalin karbar kyauta.

Domin tunawa da wadanda suka zama zakara har abadin abada, aka gina wani mutum-mutumi ga wanda ya taba zama zakara har sau uku a gidan gunki na Olympic bayan an gama gasa ta taron wasannin Olympic na can can zamanin da. Wadanda suka gina mutum-mutumin, akasarinsu mashahuran masaka ne a wancan zamani. A sa'I daya kuma, fararen hula na can can zamanin da na Girka sun mayar da 'yan wasa da suka ci nasara a gun gasanni a matsayin gumaka. Wani lokaci, idan an yi fama da bala'I daga indallahi, to wassu fararen hula sukan yi addu'a a gaban dakin gunki domin neman kiyayewa.( Sani Wang)