Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-28 11:00:08    
Bayanin Gwamnatin kasar Sin kan zaman rayuwar mata da yara (babi biyu)

cri

A shekarar bara , kasar Sin ta ci gaba da karfafa tabbacin dokokin shari'a don kiyaye ikon mata da yara . Bayan da aka gyara dokar kiyaye iko da moriyar mata da yara , daga ran 15 ga watan Disamba na wannan shekara, Dokar za ta fara aikinta . Ban da wannan kuma za a kara kudin inshora na mata wadanda suka yi haihuwa . Yawan kudin inshora ya karu da kashi 16 cikin 100 bisa na shekarar 2004 . Ma'aikatun kiwon lafiya sun kai kudin agaji ga mata masu juna biyu matalauta dubu daruruka . Ma'aikatun ba da ilmi sun mai da yawan maraya wadanda suke karatu a makaranta ba tare da biyan kudi ba ya karu da kusan kashi 93 cikin kashi 100 .

Bisa shirin da Kungiyar kiyaye ikion mata da yara ta kasar Sin ta tsara , an ce , a cikin lokacin Shririn shekaru 5-5 na 11 don raya kasar , kasar Sin za ta ci gaba da karfafa aikin tsara dokar shari'a kan kiyaye iko da moriyar mata da yara . Sa'an nan kuma za a kyautata aikin tafiyar da dokar , ta yadda za a kafa yanayin girmama mata da kiyaye moriyar yara .

Nan gaba hukumomin kiwon lafiya na kasar Sin za su ci gaba da karfafa aikin kula da mata da yara don tabbatar da sabuwar dokar .

Mr. Dai , shugaban Kungiyar hadingwiwar mata ta kasar Sin ya jaddada cewa , za mu yi kokari don mai da aikin yara da mata da ya zama muhimmin aiki kuma mai kasance da muhalli mai kyau da kuma tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci . Shugaban Kungiyar ya karfafa magana cewa , kwamitin jam'iyyar da gwamnatin jama'a sun tsai da kudurin cewa , za a rage yawan nuna bambanci ga mata da yara. Dole ne bangarori daban daban da hukumomi daban daban na gwamnatocin matakai daban daban su tabbatar da wannan kudurin a cikin manyan ayyukansu .

Bisa shirye-shiryen da aka zartas , an ce , a cikin shekaru 5 masu zuwa , yawan madaidaicin karuwar tattalin arzikin birnin Beijing na shekara-shekara zai kai kashi 9.5 cikin 100 . Kuma an tabbatar da aikin kiyaye ikon mata da yara . A cikin shekaru 5 masu zuwa , aikin kiyaye hakkin yara da mata zai ciyar da yalwatuwar unguwoyi da gundumomi cikin daidaici , za su zama tsarin musamman da manyan ayyukan birnin Beijing .

Jama'a masu sauraro , yanzu sai ku 'dan shakata kadan, daga basani kuma za mu dawo domin karanta shirinmu na Me ka sani game da kasar Sin .

Mr. Dai ya bayyana cewa , a cikin shekaru 5 da suka shige , mun dauki aikin kiyaye shahararrun lambobin kasuwanci na matan kasashen waje kamar wani muhimmin aiki na birnin Beijing na kasar Sin . Musamman ma daga shekarar 2005 zuwa karshen watan Nuwamba na wannan shekara , Ofishin lambobin kasuwanci da Kwamitin duba lambobin na hukumar sun yi amincewa da shahararrun lambobin kasuwanci na mata guda 30 na kasashen waje ciki har da Beauty Parlours da Dimond .

Kasar Sin tana daya ce daga cikin kasashe masu fama da lambobin jebu a duniya . Bayan da aka shiga sabon karni , kasar Sin ta dauki matakan magance laifufkan kera lambobin jebu na mata .

A gun taron manema labarun da Ofishin watsa labaru na Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 12 ga wata a nan birnin Beijing , Li Dongsheng , shugaban Hukumar kula da aikin mata da yara ta birnin Beijing ya ce , kasar Sin ta yi na'am da wadannan shahararrun lambobin kasuwanci kuma tana kiyaye ikon mata da yara , ta sami yabo sosai daga masana'antu masu yawa musamman ma wasu manyan kamfanonin ketare kuma sun karfafa amincewar aikin kiyaye ikon mata da yara na kasar Sin . Saboda haka , kasar Sin ta jawo hankulan kasashe masu yawa su zo nan kasar Sin don rajista lambobinsu musamman ma na mata da na yara.(Ado)