Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-27 20:04:44    
Samun bunkasuwar dantankatar da ke tsakanin zirin Taiwan ya zama sakamakon da 'yan uwa na gabobin biyu suka samu cikin hadin gwiwa

cri

A ran 27 ga wata a birnin Beijing, kakakin ofishin harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Li Weiyi ya bayyana cewa, samun bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin bangarori biyu na zirin Taiwan ya zama sakamakon da 'yan uwa na gabobin biyu suka samu cikin hadin gwiwa, bayan da suka yi fama da 'yan a-ware na Taiwan wadanda ke neman kawo baraka ga kasar Sin.

Mr Li ya bayyana cewa, a cikin wadannan shekaru 6 da Chen Shuibian yake mulki a lardin Taiwan, ya kan sanya tarnaki ga mu'amalar da gabobin biyu suka yi, kuma ya kawo cikas ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu sosai. Mr Li ya sake nanata cewa, kara yin mu'amala da hadin kai a tsakanin gabobin biyu a fannoni daban daban da kara samun bunkasuwar dangantakarsu da kara moriyar juna da samun albarkatu tare, wannan ya zama buri daya na 'yan uwan gabobin biyu da matakai da suke daukawa, wannan kuma ba za a iya hana shi ba.(Danladi)