Jama'a masu karatu, muna muku godiya da sauraren shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici wato 'Garin Panda, lardin Sihuan'. A cikin shirin musamman namu na karshe, za mu tabo magana dangane da dabbar Panda, wata alama ce ta lardin Sichuan. Za mu kai ziyara ga gandun daji na Wolong. Kafin mu soma shirinmu na yau, sai tambayoyi 2 da muka yi muku, da farko a wane lardi ne garin Panda yake? Na biyu kuma Panda nawa ne suke zama a cikin kunkurmin daji na gandun daji na Wolong?
Gorori kwarra na yin yalwa a cikin gandun daji na Wolong na lardin Sichuan. Panda, wadda wata irin dabba ce mai daraja kuma mafi dogon tarihi a duniya suna zama lami lafiya a nan.
Gandun daji na Wolong da ke arewa maso yammacin lardin Sichuan na kasar Sin na daya daga cikin manyan wuraren da Panda ke zama. Shi ya sa aka mayar da lardin Sichuan tamkar garin Panda. Masu yawon shakatawa wadanda suke son ganin Panda su kan zabi cibiyar kula da Panda ta kasar Sin da ke cikin wannan gandun daji. Zhang Liming, mai kula da gandun daji nan, ya yi karin haske cewa,
'Manufar da gandun dajinmu ke bi ita ce tabbatar da ganin cewa, Panda za su ci gaba da kasancewa lami lafiya, da kuma bai wa masu sha'awar Panda na duk duniya wata damar taba Panda kai tsaye. Ban da wannan kuma, muna gaya wa masu yawon shakatawa dalilin da ya sa ake kiyaye muhalli da tarihin Panda, muna fatan za mu fahimci muhimmancin Panda a matsayin wata irin dabba mai dogon tarihi a lokacin da suke kallonsu.'
Tun da can, mutane sun nuna sha'awa sosai kan Panda saboda jikinta ya yi kama da wani kwallo, ta kan nuna alamu masu kyau, kuma tana da gashi baki da fari. Yanzu ana kiwon Panda fiye da 100 a cikin cibiyar kula da Panda ta kasar Sin. Suna jin dadin zaman rayuwarsu sosai a nan.
Abin da ya fi jawo hankulan mutane shi ne abincin da ake bai wa Panda. Masu kiwon Panda sun yi bayanin cewa, da can Panda na cin nama, amma sun mayar da gorori a matsayin abincinsu a maimakon nama sannu a hankali. Shiyyar Wolong ta cancanci gorori da su zama sosai, shi ya sa Panda suke zama a nan. Ko da yake ba su ci gaba da cin nama ba, amma Panda ba su kyautata kwarewarsu ta hadiye ba. Shi ya sa Panda ba su motsa jiki da yawa ba, kuma su kan yi abubuwa sannu-sannu don kiyaye karfinsu.
Madam Rebecca Haase ta kasar Amurka ta dauki hotuna masu yawa kan Panda, ta yi zumudi sosai saboda ganin Panda a kusa da su sosai. Ta ce,
'Na ji farin ciki sosai saboda ganin Panda a nan, suna da kyan gani, kuma suna da lafiya. Ina fatan za a kara samun Panda a Wolong.'
An gina wani dakin zamani don kiwon kananan dabbar Panda a wannan cibiyar kula da Panda, inda mutane suka ciyar da Panda jarirai don rage yawan mutuwar Panda jarirai.
Saboda masu yawon shakatawa da yawa sun nuna sha'awa kan Panda kwarai, shi ya sa da yawa daga cikinsu suka fi son zama masu aikin sa kai a Wolong. Madam Kodama Midori, wadda ta zo daga kasar Japan na daya daga cikin irin wadannan masu aikin sa kai. Ta gaya mana cewa, abokanta 3 da ita sun zo Wolong za su yi mako daya suna zama tare da Panda. Ta ce,
'A ko wace rana da safe, na bai wa Panda abinci, na kan share dakunansu da kuma kawar da kashinsu da tsakiyar rana da kuma da yamma. Ba zai yiwu ba in zama tare da Panda a kusa haka a zaman yau da kullun, shi ya sa na ji zumudi kwarai da gaske a wannan karo.'
A zarihi kuma, masu yawon shakatawa sun iya ganin yadda Panda suka yi girma a lokuta daban daban na ko wace shekara. A lokacin zafi, Panda masu ban sha'awa cike suke da karfi sosai saboda babu zafi a Wolong. A lokacin kaka, masu yawon shakatawa sun sami damar ganin yadda Panda mata ke haihuwa 'ya'yansu, a lokacin bazara kuwa, balagaggun Panda su kan yi barbara a ko ina.
Ban da Panda da mutane suke kiwo, Panda fiye da 100 suna zama a cikin kunkurmin daji na gandun daji na Wolong a yanzu, wadanda yawansu ya kai misalin kashi 10 cikin dari da na dukan wadanda ke zama a cikin kunkurmin daji na duniya. Da can an haramta masu yawon shakatawa da su shiga cikin wuraren da wadannan Panda ke zama, amma a kwanan baya, gandun daji na Wolong ya gabatar da wani shirin shakatawa domin manyan masu yawon shakatawa. Manyan masu yawon shakatawa suna iya kallon Panda wadanda ke zama a kunkurmin daji ta hanyar tsarin sa ido na zamani.(Tasallah)
|