A yayin da shekara ta 2006 ke dab da karewa, kuma shekara ta 2007 take zuwa, me kuke tunani? Idan mun tuna, me ya fi burge ku a shekara ta 2006 wadda ke karewa, kuma mene ne fatanku ga sabuwar shekara? Ko kuna da abin da kuke son fada? A hakika, kwanan nan, masu sauraronmu da yawa sun rubuto mana wasiku, inda suka fada mana abubuwan da suka fi burge su a shekara ta 2006 da kuma fatansu ga shekara ta 2007.
Malam Djibo Hamza daga birnin Yamai, jamhuriyar Nijer ya rubuto mana cewa, shekara kwance in ji Hausawa kwana na bin kwana, yau Allah ya kawo mu karshen shekarar 2006, sai dai ni babban abin da ya fi burge ni a wannan shekara shi ne irin yadda na samu damar kulla alaka da mutane daban daban a sassan duniya daban daban ta hanyar internet, wanda gidan rediyon CRI na daya daga cikinsu, wanda hakan abin alfahari ne a gare ni. Sa'an nan, babban burin da na ke da shi a shekara ta 2007 shi ne in yi aikin hajji tare da ziyartar birnin Madina. Sa'an nan kasar China na daya daga cikin kasashen da nake begen ziyarta musamman don na ga babbar ganuwar kasar Sin, da fatan wannan mafarki nawa zai zama gaskiya. To, gaskiya buri ne mai kyau, mu ma muna rokon Allah don ya cika burinka a sabuwar shekara.
Sai kuma malam Abba Garba daga Gumel, jihar Jigawa ta tarayyar Nijeriya ya ce, fatana a sabuwar shekara shi ne a samu dawamammen zaman lafiya a gabas ta tsakiya.
Malam Sanusi Isah Dankaba daga birnin Keffi, jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, ina farin cikin taya murnar sabuwar shekara ta dubu biyu da bakwai mai kamawa ga sashen hausa na gidan rediyon kasar Sin, tare da yan uwana masu sauraron cri a duk inda suke a duniyar nan. Allah ya maimaita mana na badin badada. A kowace shekara mai karewa, dole ne a samu abubuwan ban al-ajabi da ya faru a wannan duniyar tamu, haka ma duk shekara mai kamawa duk wani mahaluki mai nunfashi zai iya hasashen abun da yake tunani ko bukata a sabuwar shekara. A shekarar da ta gabata, wato shekarar 2006 akwai wadansu abubuwa wadanda ba zan taba mantawa da su ba, alal misali kamar shagulgulan biki da tashar rediyon cri ta yi na murnar cika shekaru sittin da biyar da kafuwar gidan radiyon kasar Sin wanda shi ne babban abun da nike tunawa da shi ta harkar kasashen waje. Bayan haka kuma ina matukar murna da shigowar wannan sabuwar shekara ta 2007 tare da fatan Allah ya sa in samu nasarar gasar kacici kacici ta garin panda wanda gidan rediyon kasar Sin ya shirya a kan lardin Sichuan na kasar Sin, saboda kullum burina shi ne wannan shekara ta 2007 in ziyarci wata kasar ta waje musamman kasar yankin Asia wanda take da nisa da kasa ta Nigeria, bugu da kari ina fatan alheri tare da fatan wadansu matsaloli da ake fama da su a wadansu yankuna na duniya allah ya kawo karshen warware wadannan matsaloli, alal misali kamar maganar nuclear ta korea ta arewa da ta kasar Iran da rikicin kasar Somalia da Iraq da Afghanistan da dai sauransu. Daga karshe ina isar da gaisuwata ta taya murnar sabuwar shekara ta 2007 ga dukkanin ma'aikatan gidan rediyon kasar Sin, Allah ya maimaita mana amin.
Har wa yau kuma, malam Abba Mohammed, daga Kano, Nijeriya ya rubuto mana cewa, abin da ya fi burge ni a shekara ta 2006, shi ne taron da kasar Sin ta yi da kasashen Afrika. Sabo da Kasar Sin ta nuna wa duniya cewar tana nan tare da mutanen Afrika, za ta kuma ci gaba da tallafa musu ta ko wace fuska. Sa'an nan fatana a shekarar 2007, shi ne a yi zabe lafiya a kasa ta Nijeriya, Allah ya sa a yi shi lafiya.
Akwai kuma malam Sanusi Musa Chimas daga Isyaku Road Fayamas, Malumfashi, jihar Katsina, Nijeriya, da kuma malam Salisu Usman daga ABU, Zaria, Nijeriya, da dai sauran masu sauraronmu da suka mika mana gaishe-gaishensu na sabuwar shekara ga dukan ma'aikatan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, mun gode, mu ma muna muku fatan alheri na sabuwar shekara.
A hakikanin gaskiya, wasikun masu sauraronmu sun burge mu kwarai da gaske, musamman fatansu na alheri ga sabuwar shekara, a nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, mu ma muna fatan kome zai tafi daidai tare da ku masu sauraronmu a sabuwar shekara, Allah ya cika duk kyakkyawan burin da kuke da shi, kuma Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu da masu sauraronmu. (Lubabatu)
|