Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-27 16:50:56    
Aikin samar da bayanan albarkatun al'adu cikin hadin guiwa ya kawo alheri ga mazaunan birane da kauyuka na kasar Sin

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, mutane suna kan tabo magana a kan batun ratar da aka samu a birane da kauyuka a lokacin da ake raya su. Ba ma kawai irin ratar tana bayyanu a kan matsayin raya tattalin arziki da sayen kayayyaki na yau da kullum ba, hatta ma tana bayyanu wajen kashe kudade don more rayuwa a fannin al'adu. A cikin wasu shekarun da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta yi gwajin yin amfani da kimiyya da fasaha na zamanin yau don rage ratar da ke tsakanin birane da kauyuka wajen kashe kudade don more rayuwa a fannin al'adu, amma wane irin hali ne ake ciki yanzu a fannin nan?

Garin Sancha shi ne karamin gari da ke nisa da birane a gundumar Zhunyi ta lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Kafin shekaru biyu da suka wuce, cikin hadin guiwa ne ma'aikatar al'adu da ta kudi da sauran ma'aikatu da kwamitoci na kasar Sin sun kafa wata tashar samar da hidima ga kananan hukumomi wajen samar da bayanan al'adu na duk kasa ga kowa. An mika wa tashar wani inji mai kwakwalwa wato kumputer da wani injin nuna film da wasu ajiyayyun takardun kidaya. Daga nan, tashar nan ta zama wani wurin da mazaunan wurin suke taruwa a cunkushe. Shugaban tashar Luo Gang ya bayyana cewa, tasharmu wata cibiya ce ta hada da duk garinmu tare da mutane dubu 30, in wani kauye ko wani rukunin kauyawa suna bukatar hidimarmu, to hukumar garin tana iya aika motar da ke dauke da mu, mu isa kowane wuri ko kowace farfajiyar gidan manoma tare da kumputermu don samar da hidimarmu gare su, wato samar musu labarai dangane da kimiyya da fasaha na ayyukan noma, kamar yadda ake noman shuke-shuke da kiwon dabbobi da sauransu, jama'ar wurin suna karbuwar mu sosai da sosai.

Yanzu, a duk kasar Sin, da akwai irin wadandan tashoshi dubu 6, wannan ne wani kashi da ke cikin ayyukan gwamnatin kasar Sin wajen samar da labaran al'adu ga duk kasa.

Mataimakin ministan al'adu na kasar Sin Zhou Heping ya bayyana cewa, ayyukan al'adun kasar Sin suna baya baya, kuma halin da ake ciki na rasa daidaituwa a tsakanin shiyya shiyya ya kawo cikas sosai ga yada labaran al'adu , musamman ma dimbin jama'a ba su da saukin samun damar karanta littattafai, musamman ma jama'ar da ke zama a wuraren da ke nisa da birane suna kara shan wahalhalu a fannin nan. Saboda haka gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali ga aiki nan na da muhimmanci sosai.

Mr Zhang Yanbo shi ne direktan cibiyar samar da labaran al'adu ga kowa ta kasar Sin, ya bayyana cewa, ga wani misali da aka bayar, an ce, birnin Shanghai na kasar Sin ya shimfida tsarin tashoshin internet a duk unguwanninsa ta hanyar tashar samar da labaran birane don yada duk albarkatan bayanan al'adu da ke hannunsa. Ta hakan, ana kara biyan bukatun mazaunan unguwannin birnin wajen samun ilmi da jin nishadin saurarar shirye-shiryen wake-wake da raya-raye da kallonsu, a birnin Qingdao na lardin Shandong da birnin Foshan na lardin Kwangdong, mazaunan da yawansu ya kai dubu 800 suna iya samun labaran al'adu a cikin gidajensu.

Mr Zhang Yanbo ya bayyana cewa, a bayyane ne jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke rike da mulkin kasa ta yi niyyar kafa zamantakewar al'umma mai jituwa da kuma kara kyautata ayyukan al'adu da ke da nasaba da moriyar jama'a, amma aikin samar da labaran al'adu ga kowa shi ne mataki mai muhimmanci da ake yi a cikin ayyukan. Wato gwamnati ta ware kudade don samar wa mazaunan birane da kauyuka labaran da suke bukata, wannan na da ma'ana mai muhimmanci ga kara kyautata abubuwan al'adu ga mutane da kafa zamantakewar al'umma mai jituwa.(Halima)