Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-27 16:48:30    
Kasar Sin tana raya sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu lami lafiya

cri
Ran 20 ga wata, Hadaddiyar Kungiyar Harkokin Nakasassu ta kasar Sin ta sanar da cewa, ana shirya taron wasannin motsa jiki na nakasassu na kasar Sin a karo na 7 lami lafiya, yanzu an kusan bude wannan taro. Taron wasannin motsa jiki na nakasassu na wannan karo taron wasannin motsa jiki ne mafi girma da kasar Sin za ta shirya domin jama'arta nakasassu kafin taron wasannin Olympic na nakasassu na shekara ta 2008 na Beijing. Mataimakiyar darektar sashen wasannin motsa jiki na Hadaddiyar Kungiyar Harkokin Nakasassu ta kasar Sin madam Zhao Sujing ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin da zaman al'ummar kasar suna mai da hankulansu da kuma dora muhimmanci kan sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu na kasar Sin, shi ya sa wannan aiki yana samun ci gaba.

Madam Zhao ta yi karin haske cewa, nakasassu fiye da miliyan 80 ne suke zama a kasar Sin a yanzu, saboda hadaddun kungiyoyin harkokin nakasassu na wurare daban daban na kasar suna tafiyar da ayyukansu, haka kuma rukunnoni daban daban na zaman al'ummar kasar suna mai da hankulansu a kan nakasassu, nakasassu da yawa suna motsa jiki don kara karfin jikuna cikin himma da kwazo. An fito da tsarin shirya wasannin motsa jiki domin nakasassu a kasar Sin. Kasar Sin ta riga ta kira tarurukan wasannin motsa jiki na nakasassunta sau da yawa a jere bisa wannan tushe. Ta ce,'Yanzu kasarmu ta ci nasarar shirya tarurukan wasannin motsa jiki na nakasassu nata har sau 6, za a yi irin wannan kasaitaccen taro a karo na 7 a lardin Yunnan a watan Mayu mai zuwa. Yawan gasannin wannan muhimmin taro ya karu zuwa 20 na yanzu, a maimakon gasanni 3 kawai na da, ana raya irin wannan sha'ani na duniya, a lokaci daya kuma, kasar Sin tana raya wasannin motsa jiki na nakasassu. A kan yi taron wasannin motsa jiki na nakasassu na kasar Sin sau daya a ko wadanne shekaru 4, wanda aka tanade shi a cikin jerin manyan tarurukan motsa jiki da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta zartas da su. Kasar Sin ta riga ta fito da tsari da ka'idoji kan raya sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu.'

A lokacin da take tafiyar da harkoki da tarurukan wasannin motsa jiki na nakasassu a duk kasar, a sa'i daya kuma, kasar Sin tana shiga cikin wasannin Olympic na nakasassu na duniya cikin himma da kwazo, ta kuma sami maki mai kyau.

Yanzu an rage lokaci kadan da za a bude taron wasannin Olympic na nakasassu a nan Beijing a shekara ta 2008, madam Zhao ta yi bayanin cewa, shirya wannan muhimmin taro ya daukaka ci gaban sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu na kasar Sin, saboda haka, rukunoni daban daban na zaman al'ummar kasar Sin sun kara mai da hankulansu kan sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu. Ta yi karin haske cewa,'Da farko dai, ba kamar yadda aka yi a da ba, yanzu larduna da birane da yawa na kasarmu sun fara gina sansanonin horo da filayen wasa, wadanda nakasassu za su iya yin amfani da su cikin sauki. Ba a gina wani sabon sansani ba, a maimakon haka, an yi kwaskwarima kan sansanoni na yanzu ta fuskar kawar da shinge don biyan bukatun nakasassu, ta haka nakasassu suna iya motsa jiki a cikin wadannan sansanoni tare da sauran mutane cikin sauki, wadanda suke kusa da gidajensu.'

Ko da yake ta samu ci gaba a fannoni da yawa, amma kasar Sin wata kasa ce mai tasowa, kuma ba ta dade tana raya sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu ba, a sakamakon haka, kasar Sin tana fuskanta batutuwa da yawa wadanda dole ne ta kyautata su da kuma daga matsayinsu. Madam Zhao tana ganin cewa,'Saboda kasarmu ba ta dade tana bunkasa sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu ba, kuma tushen wannan sha'ani ba ya da inganci sosai, shi ya sa taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing na shekara ta 2008 ya kawo mana sabbin kalubale, kamar su, wasannin motsa jiki na jama'a na nakasassu yana baya-baya, wannan ya kawo illa ga kafa kungiyoyin wakilai da kuma zaben 'yan wasa nakasassu domin taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing na shekara ta 2008 kai tsaye, haka kuma ya kawo illa ga dauwamammiyar bunkasuwar sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu na kasarmu.'

Nakasassu da yawa suna motsa jiki don kara karfin jikunansu, ta haka za a kyautata ingancin jikunansu da kuma karfafa aniyarsu ga zaman rayuwa, wannan babban makasudin Hadaddiyar Kungiyar Harkokin Nakasassu ta kasar Sin ne da ta daukaka ci gaban sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu. Madam Zhao ta yi imanin cewa, babban tasirin da taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing zai bayar zai sanya dukan rukunonin zaman al'ummar kasar Sin su kara mai da hankulansu kan sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu, sa'an nan kuma, nan gaba nakasassun kasar Sin za su sami sharudda masu kyau wajen motsa jiki, za su kuma kara motsa jiki a sakamakon karfafa gwiwar da taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing zai yi musu.(Tasallah)