Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-27 16:48:30    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(21/12-27/12)

cri
Ran 19 ga wata, a birnin Kuala Lumpur, hedkwatar kasar Malaysia, an yi bikin jefa kuri'a cikin kungiya kungiya domin gasar cin kofin Asiya ta wasan kwallon kafa ta shekara ta 2007. An raba kungiyoyi 16 masu shiga wannan gasa zuwa rukunoni 4. An mayar da kungiyoyin kasashen Australia da Iran da Japan da kuma Korea ta Kudu tamkar gogaggun kungiyoyi. Kungiyar kasar Sin da kungiyoyin kasashen Iran da Malaysia da kuma Uzbekistan suna cikin rukuni na C. Za a yi wannan muhimmiyar gasa a kasashen Malaysia da Thailand da Indonesia da kuma Viet Nam tare a watan Yuli mai zuwa.

Tun daga ran 20 zuwa ran 21 ga wata, aka yi gasar fid da zakara ta wasan kwallon tebur ta duniya a karo na farko a Changsha na kasar Sin. Dan wasa Wang Liqin na kasar Sin da 'yar wasa Zhang Yining ta kasar Sin sun zama zakaru a cikin rukunoni na maza da na mata. Dukan 'yan wasa maza 8 da mata 8 da suka shiga wannan gasa su zakaru ne a cikin manyan gasannin wasan kwallon tebur na duniya da kuma wadanda suke kan gaba a cikin jerin sunayen 'yan wasan kwallon tebur na duniya.

Ran 21 ga wata, Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA ta gabatar da jerin sunayen kungiyoyin wasan kwallon kafa na mata na kasashen duniya na shekara ta 2006. Kasashen Jamus da Amurka da kuma Norway sun zama na farko da na biyu da kuma na uku, kasar Sin kuwa ta zama ta 9, kamar da yadda take a cikin wannan jerin sunaye a shekara ta 2005.

Ban da wannan kuma, a kwanan baya, a birnin Zurich na kasar Switzerland, kungiyar FIFA ta sanar da cewa, dan wasan kwallon kafa Fabio Cannavaro na kasar Italiya da kuma sabuwar 'yar wasan kwallon kafa Marta ta kasar Brazil sun zama nagartattun 'yan wasan kwallon kafa na duniya na shekarar 2006.

Ran 22 ga wata, kwamitin wasan Olympic na duniya wato IOC ya bayyana cewa, ya gamsu da ci gaban da kasashen Korea ta Arewa da Korea ta Kudu suka samu game da batun kafa hadaddiyar kungiya don shiga taron wasannin Olympic da za a yi a Beijing a shekara ta 2008, ya kuma sa ran alheri domin ganin wadannan kasashe 2 za su kafa hadaddiyar kungiya za su shiga taron wasannin Olympic na Beijing tare. A farkon wannan wata, wakilan kasashen Korea ta Arewa da Korea ta Kudu sun tattauna wannan batu a gun taron wasannin motsa jiki na Asiya na Doha.(Tasallah)