Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-26 16:01:55    
Fitsarin kwance wani irin ciwo ne da zai iya warkewa da kansa

cri

Yin fitsarin kwace ba abin mamaki ba ne ga yara. Sa'ilin da yara suka kai shekaru biyu da haihuwa, su kan daina yin fitsarin kwance, amma wasu yaran su kan ci gaba da yin fitsarin kwance har zuwa shekaru biyar da haihuwa ko kuma sama da haka. Domin kuwa akwai yaran da yawansu ya kai kashi 5 cikin dari su kan ci gaba da yin fitsarin kwance har zuwa shekaru 10 da haihuwa, kadan ne daga cikinsu kuwa su kan yi haka har lokacin kuruciya. Dr. Anubala, wani shahararren likita na kasar Indiya ya nuna cewa, kwayoyin halitta wato "Gene" a turance shi ne muhimmin sanadin da ke haifar da fitsarin kwance ga yara, amma ana iya magance matsalar ta ilmantar da su ta hanyoyi daban daban.

Bisa labarin da jaridar mabiya addinin Hind ta kasar Indiya ta bayar a kwanakin nan, an ce, Dr. Anubala wanda ya taba yin aiki a cibiyar nazarin lafiyar yara ta gwamnatin kasar Indiya ya nuna cewa, idan daya daga cikin iyayen yara ya taba kasancewa mai yin fitsarin kwance a lokacin yarantakarsa, to yiyuwar yin fitsarin kwance ga yara za ta kai kashi 40 cikin dari. Kuma idan dukkan iyayen yara sun taba yin fitsarin kwance a lokacin yarantakarsu, to yiyuwar yin fitsarin kwance ga yara za ta kai kashi 70 cikin dari. Bugu da kari kuma Dr. Anubala ya bayyana cewa, akwai dalilai masu yawa da za su haifar da matsalar fitsarin kwance, kamar kwayoyin halitta, da yin numfashi ta baki yayin barci, da kuma rashin samun barci yadda ya kamata da dai sauransu.

Haka kuma Dr. Anubala yana ganin cewa, wasu iyayen yara da ke nuna damuwa sosai kan matsalar fitsarin kwance sun kambama matsalar. Bai kamata su matsawa yaransu ba, sabo da idan suka yi haka, to za su sanya yaran cikin damuwa, ta haka yaran za su dauka tamkar sun yi wani babban laifi. Dole ne iyaye su fahimta cewa, za a iya magance matsalar fitsarin kwance, kuma ya kamata su nuna goyon baya ga yaransu wadanda ke cikin wannan mawuyacin hali.

Ban da wannan kuma ya gano cewa, ilmantar da yara yadda ya kamata a fannin halin rayuwa za ta bayar da taimako sosai ga yara. Alal misali, ya kamata a horar da yara wajen yin fitsari yadda ya kamata, da kayyade yara wajen shan ruwa kafin barci, da yin fitsari kafin su yi barci, da kuma yin fitsari na lokaci-lokaci wanda ya fi ba da taimako ga yaran da shekarunsu ya yi yawa a gwargwado, sabo da ba safai su kan yi fitsari har awoyi da dama ba lokacin da suke yin wasa tare da abokansu.

Kuma Dr. Anubala ya bayyana cewa, ba a bukatar magance matsalar fitsarin kwance ta hanyar jiyya. Idan iyaye suka yi hakuri na wani lokaci, to ciwon zai iya warkewa da kansa.(Kande)