Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-26 15:59:22    
Bakin teku wurin shakatawa na Yalongwan

cri

Bakin teku wurin shakatawa na Yalongwan wani sharararren wurin shakatawa ne da ke birnin Sanya na lardin Hainan na kasar Sin, wanda ke da nisan misalin kilomita 25 daga birnin Sanya. Bayan hukumar wurin ta yarda da shirin da aka bayar, an kafa wurin 'yan yawon shakatawa na kasar Sin a Bakin teku wurin shakatawa na Yalongwan a ran 2 ga watan Oktoba na shekara ta 1992. A duk fadin kasar Sin, sai a cikin wannan wurin 'yan yawon shakatawa ne kawai masu yawon shakatawa suke iya kallon wurare masu ni'imma irin na wurare masu zafi.

Hukumar birnin Sanya ta yarda da kamfanin raya bakin teku wurin shakatawa na Yalongwan da ya bunkasa wannan wurin shakatawa. Kamfanin nan ya ba da babbar gudummawa wajen raya bakin teku wurin shakatawa na Yalongwan a matsayin babban wurin 'yan yawon shakatawa wanda ya yi suna a duk duniya.

A shekarun nan da suka shige, wannan kamfani ya zuba kudi da yawa don kyautata gine-gine da manyan ayyuka a wurin. Saboda kyautatuwar yanayi ta fuskar zuba jari a nan, an samar da sabbin gine-gine da hotel da wurare masu ni'ima don kara jawo masu yawon shakatawa.

A cikin wadannan sabbin gine-gine, dandalin tsakiya na bakin teku wurin shakatawa na Yalongwan mai fadin misalin murabba'in mita 70,000 ya fi shahara. Ya yi kama da wata alama ce ta wannan wurin 'yan yawon shakatawa. A tsakiyarsa, an sami wani babban ginshiki da aka yi da dutse, tsayinsa ya kai misalin mita 26.8, inda aka sassaka almara da tatsuniyoyi na zamanin da na kasar Sin.

Ban da wannan kuma, akwai sauran wurare da suka cancanci masu yawon shakatawa da su kai ziyara, kamar su, babban dakin nune-nunen bawo da kwarin malam-bude-littafi. Sa'an nan kuma, mutane suna iya yin alkahura a cikin ruwa da tukin kananan jiragen ruwa da kuma wasan tseren ruwa da sauran wasannin motsa jiki kan ruwa masu ba sha'awa.

Bakin teku wurin shakatawa na Yalongwan mai fadin murabba'in kilomita 18.6 yana jawo masu yawon shakatawa da yawa daga wurare daban daban.(Tasallah)