Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-25 15:59:45    
Kasar Sin za ta daga matsayin hadin gwiwa tsakaninta da kasashen waje a fannin kimiyya da fasaha daga dukkan fannoni

cri

A 'yan kwanakin nan da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta bayar da tsarin aikace-aikace wajen hadin gwiwa tsakaninta da kasashen waje a shekaru biyar masu zuwa, kuma ta gabatar da wani shiri kan kara bude kofa ga kasashen waje don tsara sabon tsarin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa wajen kimiyya da fasaha bisa halin da kasashe da shiyya-shiyya da kuma kungiyoyin kimiyya da fasaha na duniya daban daban suke ciki, ta yadda za a iya daga matsayin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen waje a fannonin kimiyya da fasaha. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wannan batu.

Ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Xu Guanhua ya yi muku bayani kan wannan tsarin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen waje kan kimiyya da fasaha, cewa,

"kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Turai da Amurka da Japan da Korea ta Kudu da dai sauransu domin neman samun sakamako mai kyau a fannonin muhimmin nazari da fasahohin zamani, kuma za ta kara hadin kai tare da kungiyar tarayyar kasashe masu 'yancin kai da kasashen Indiya da Brazil a fannoni da yawa domin taimakon juna da kuma samun bunkasuwa tare. Ban da wannan kuma kasar Sin tana dora muhimmanci kan hadin gwiwa tare da kasashen Asiya da Afirka a fannin kimiyya da fasaha domin kara ba da taimako da shirya kwas din horaswa kan kimiyya da fasaha ga kasashe masu tasowa. A waje daya kuma tana mai da hankalinta wajen hadin gwiwa da yin mu'amala tsakaninta da kungiyar tarayyar Turai da ta ASEAN da kuma kungiyar makamashin nukiliya ta duniya."

Bisa abubuwan da aka tanada a cikin tsarin aikatawa wajen hadin gwiwa tare da kasashen waje a nan gaba, an ce, game da hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashe da kungiyoyin duniya da abin ya shafa, kasar Sin za ta mayar da raya makamashi da albarkatun ruwa da kuma kare muhallin halittu a gaban kome yayin da za ta dora muhimmanci kan tabbatar da ingancin abinci da kyautata tsarin albarkatun gona da kuma daga matsayin lafiyar fararren hula.

Jihar Shandong da ke gabashin kasar Sin tana daya daga cikin yankunan da suka himmantu kan hadin gwiwa tare da kasashen waje a fannin kimiyya da fasaha. Madam Zhai Luning, mai kula da ayyukan kimiyya da fasaha na jihar ta bayyana cewa, ta yin hadin gwiwa tare da kasashen waje kan kimiyya da fasaha, an daga matsayin kwarewar jihar wajen kirkire-kirkire, a waje daya kuma an sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta bangarorin da suka shiga ayyukan hadin kai. Kuma ta ce,

"a shekaru biyar da suka gabata, jihar Shandong ta sa hannu a cikin aikace-aikace 12 na tsarin shiri na kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai, daya daga cikinsu shi ne ta hada kanta tare da wata cibiyar nazari ta kasar Jamus wajen raya ayyukan tsabtataccen makamashi da aka samu daga halittu. Da farko jihar Shandong ta zuba jari na EURO miliyan 30, a cikin shekara guda an samar da danyen man halittu ton dubu 50 da kuma man dizal da ke kunshe da man halittu mai inganci da yawansu ya kai ton dubu 10."

Ban da wannan kuma jihar Shandong ta hada gwiwa da yin cudanyar kimiyya da fasaha tare da kasashen Amurka da Japan da kuma membobin kungiyar ASEAN ta hanyoyi iri daban daban. Bisa labarin da muka samu, an ce, ya zuwa yanzu sauran yankunan kasar Sin suna himmantu kan hadin gwiwa tare da kasashen waje a fannin kimiyya da fasaha.

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, a shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta zuba jari fiye da kudin Sin yuan biliyan 8 wajen raya ayyukan hadin gwiwa tare da kasashen waje a fannin kimiyya da fasaha. Haka kuma an ce, a 'yan shekaru masu zuwa, kasar Sin za ta ci gaba da kara yawan kudin da za a zuba a wannan fannin, ta yadda za a iya ci gaba da daga matsayin hadin gwiwa tare da kasashen waje kan kimiyya da fasaha. Xu Guanhua, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin ya bayyana cewa,

"kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje a fannin kimiyya da fasaha, kuma za ta inganta hadin gwiwa da yin cudanya tare da kasashen waje kan kimiyya da fasaha cikin himma da kwazo don raya muhimman ayyukan kimiyya da fasaha na kasar Sin. Haka kuma kasar Sin za ta ba da taimako wajen kafuwar hukumomin nazari na hadin kai tsakanin Sin da kasashen waje, ciki har da kafa hukumar nazarin kamfanoni tare da kuma kafa wasu hadaddun sansanonin nazari a jere. Bugu da kari kuma kasar Sin za ta kara yin cudanya tsakanin masu aikin kimiyya da fasaha na Sin da na kasashen waje, ta yadda za a iya bunkasa ayyukan horo da shigad da kwararru na kasashe daban daban."(Kande Gao)