Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-25 15:56:54    
Takaitaccen bayani game da kabilar Tibet

cri

Kabilar Tibet tana daya daga cikin muhimman kabilun kasar Sin, kuma mutanen kabilar suna da zama a babban tudun Qinghai-Tibet, wato yawancinsu suna da zama a jihar Tibet mai cin gashin kanta da wasu wurare na lardin Qinghai da na Gansu da na Sichuan da kuma na Yunnan da ke arewa da kudu maso yammacin kasar Sin. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar Tibet ya kai fiye da miliyan 5 da dubu dari 4. Kabilar Tibet tana da yare da babbaku nata.

A cikin harshen Han, wato harshen Sinanci ne ake kira ta kabilar Tibet, amma mutanen kabilar suna kiran kansu kabilar Fan. Kakanin-kakanin kabilar Tibet sun yi zama a yankunan da ke shafar kogin Yaruzanbo. Bisa ilmin tarihi da aka samu, an ce, tun yau da shekaru fiye da dubu 4 da suka wuce, kakanin-kakanin kabilar Tibet suka fara zama a yankunan da ke shafar kogin Yaruzanbo.

A karni na 13 da ya wuce, kabilar Mongoliya ta samu ikon mulkin duk kasar Sin ta kafa daular Yuan. Gwamnatin tsakiya ta daular Yuan ta kafa kananan hukumomin a yankunan da mutanen kabilar Tibet suke zama kuma ta aika da sojojinta da nada jami'ai a wadannan yankunan kabilar Tibet. Wannan ya alamantar da cewa, yankunan kabilar Tibet sun fara shiga tasiwirar kasar Sin, sun zama yankunan kasar Sin. Sa'an nan, daulolin Ming da Qing da Jamhuriyar kasar Sin da kuma Jamhuriyar Jama'ar Sin, da aka kafa bayan daular Yuan sun yi ta tafiyar da ikon mulki a yankunan kabilar Tibet.

Kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, ya kasance da tsarin mulkin kama karya da ke hada addini da siyasa a yawancin yankunan Tibet, kuma kabilar Tibet tana cikin zaman al'ummar kama karya.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, an 'yantar da yankunan Tibet bi da bi ta hanyar zaman lafiya. A ran 23 ga watan Mayu na shekarar 1953, an kulla yarjejeniyar da ke cike da sharuda 17 game da yunkurin 'yantar da yankunan Tibet ta hanyar zaman lafiya a tsakanin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da karamar gwamnatin Tibet bayan yin shawarwari a tsakaninsu. Dalai Lama da Banchanerdeni, shugabanni 2 na kabilar Tibet a wancan lokaci dukkansu sun aika da sakwanninsu ga gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, inda suke bayyana matsayinsu na amincewa da yarjejeniyar.

Bayan kafuwar jihar Tibet mai cin gashin kanta, an kafa masana'antun samar da wutar lantaki da na sarrafawa kayayyaki masu guba da na kera injuna da na hakar ma'adinai da dai makamatansu. Bugu da kari kuma, an shimfida hanyoyin mota masu dimbin yawa a jihar. A waje daya kuma, an kafa hanyar jiragen sama a tsakanin birnin Lhasa, hedkwatar jihar da birnin Beijing da sauran muhimman biranen kasar Sin. A ran 1 ga wata, an kuma kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet. Wannan hanyar dogo ta farko ce a cikin jihar.

A da, kabilar Tibet ba ta da dalibai wadanda suka gama karatu daga jami'a. Amma yanzu, an riga an kafa jami'ar Tibet a birnin Lhasa, dalibai masu dimbin yawa suna kuma yin karatu a jami'o'in sauran wuraren kasar Sin.(Sanusi Chen)