Barkanku da war haka! Yau ma ga shi Allah ya sake hada mu a wanan shiri namu mai ban sha'awa na 'wasannin Olympics na Beijing ', wanda mukan gabatar muku a kowace ranar Asabar bayan labaru. Saboda haka, sai ku karkade kunnuwanku don jin labarin da muke dauke da su a yau game da taron wasannin motsa jiki na Olympics. Daga baya ga wani bayanin musamman dangane da wasannin Olympics.
Aminai, kuna sane da cewa, a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics na can can zamanin da, akan gudanar da wasa irin na musamman, wanda ya hada da gasanni guda biyar, wato na wasan yin dogon tsalle wato long jump, da wasan jifar faifan karfe, da wasan jifar mashi, da wasan tsere da kuma wasan kokawa. Abu mai sha'awa, shi ne wassu wasanni daga cikinsu sun sha bamban da na zamanin yanzu. To, bari mu dauki wasan yin dogon tsalle a matsayin wani misali: a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics na can can zamanin da, idan kafafuwa biyu na dan wasa ba su yi kunnen doki lokacin da suka taba kasa ba, to kuwa aikin banza ne ya yi; ban da wannan kuma, akan busa sarewa lokacin da dan wasa yake shiga gasa. Muhimmin amfanin bushe-bushen sarewa, shi ne sa kuzari ga 'yan wasa da kuma kidaya sakamakon da sukan samu a gun gasa. Bugu da kari kuma, a gun taro wasannin Olympics na can can zamanin da, an tanadi, cewa wajibi ne dan wasa ya rike da wani abun da nauyinsa ya kai kilo 1.5 zuwa kilo 4.5 lokacin da yake yin tsalle.
Yanzu bari in ba ku wani labari game da wasan jifar faifan karfe. Wasan jifar faifan karfe ya zama tamkar wani irin kayan gado ne na wasan motsa jiki da aka samu daga taron wasannin motsa jiki na Olympics na Girka ta zamanin da. Nauyin faifan karfe da kuma fadin madawwarinsa da akan yi amfani da shi a gun taro wasannin motsa jiki na Olympics na zamanin yanzu, an kera shi ne daga faifan karfe guda 15 na zamanin can can da, wadanda aka hako a wurin da aka gudanar da taron wasannin motsa jiki na Olympics na tsohuwar Girka.
Jama'a masu sauraro, kuna sane da, cewa a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics na zamanin can can da, 'yan wasa sukan yi wasan jefi ne da dutse wato faifan dutse ke nan. A misalin hijira ta 6 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisalam, aka soma yin amfani da faifan karfe maimakon faifan dutse wanda yake da saukin fashewa. Har zuwa yanzu muna kiransa faifan karfe ne.
Irin wasa na uku na taron wasannin motsa jiki na Olympic na zamanin can can da, shi ne wasan jefa mashi. Tuni a cikin harkar farauta da akan yi a shekaru aru-aru da suka shige, mutane sun riga sun san darajar yin amfani da mashi. A yake-yaken da aka yi ta yi, mutanen tsohuwar kasar Girka su ma sun san darajar mashi. Saboda haka, a cikin makarantun mutanen Girka ta shekaru aru-aru da suka gabata, wajibi ne yara su yi koyon fasahohi iri daban daban na jifar mashi ko da hannun hagu da dama a lokaci daya. A gun taron wasannin Olympic na shekaru aru-aru da suka shige, tsawon mashin da 'yan wasa sukan yi amfani shi ya kai santimita 160, wanda kuma ya yi muwafaka da na balaga. Halayen musamman iri daban daban na mashin da mukan gansu a halin yanzu sun tashi da na taron wasannin motsa jiki na Olympic na can can zamanin da.
Jama'a masu sauraro, wani wasa dake cikin wasanni iri biyar na taron wasannin Olympic shi ne wasan tsere na nisan mita 192 kacal; Wasa na karshe na wasanni iri biyar na wancan zamani, shi ne wasan kokawa.
An yi wadannan wasanni iri biyar a gun taron wasannin Olympic na can can zamanin da ne bisa tsarin da aka yi na daga gasar tsere, sai dogon tsalle, sai jifar haifan karfe, sai jifar mashi sai kuma gasar kokawa. Duk wanda ya samu maki mafi kyau a cikin wadannan wasanni, shi zai zama zakara a gun gasar.
To, jama'a masu sauraronmu, mun dai karanta muku wani bayanin musamman na game da wasannin motsa jiki na Olympic. A cikin bayanin, mun ba ku labarin, cewa a gun taron wasannin Olympics na can can zamanin da, akan yi wasa irin na musamman wanda ya hada da wasanni biyar, wato na wasan yin dogon tsalle, da wasan jifar faifain karfe, da wasan jifar mashi, da wasan tsere da kuma wasan kokawa. Wasan da ya fi ba mu sha'awa, shi ne wasan yin dogon tsalle wato long jump a Turance. A gun garon wasannin motsa jiki na Olympic na can can zamanin da, idan kafufuwan
|