Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-22 13:02:18    
Fada ya sake barkewa tsakanin marikitan kasa Somaliya

cri

Kwanakin baya a jere, ana ta yin bat kashi a kasar Somaliya. Jiya ran 21 ga wata, kungiyar 'yan Islama wadda ta mallake birnin Mogadishu babban birnin kasar da kuma akasarin yankunan kasar ta yi shelar tayar da yaki ga kasar Habasha; Ban da wannan kuma wannan kungiya ta yi kira ga dukan mutanen kasar Somaliya da su tashi tsaye don shiga fada da kasar Habasha ta hanyoyi daban daban. Lallai wannan ya kara zafafa halin da ake ciki a kasar Somaliya wanda yake damun mutane.

Har kullum kasar Somaliya na cikin halin " Kara-a-zube" tun daga shekarar 1991. A shekarar 2004, an kafa gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya a kasar Kenya, wadda aka mayar da ita zuwa cikin yankin kasar a shekarar 2005. Amma har kullum gwamnatin rikon kwaryar tana gazawa wajen sarrafe-sarrafen lamuran duk kasar. Daga nasa bangaren, " Kawancen kotu ta Islama" yana ta samun karfi a 'yan watannin da suka gabata, har ya mallake birnin Mogadishu, hedkwatar kasar da kuma akasarin yankunan kasar; Amma gwamnatin rikon kwarya ta kasar tana aiki ne a wani gari kawai dake da nisan kilo-mita 250 daga arewa maso yammacin birnin Mogadishu, inda kuma takan sha kurari daga 'yan gwagwarmayar kungiyar Islama. Da yake halin da ake ciki yanzu a kasar Somaliya ya kara tsanani, shi ya sa gwamnatin rikon kwarya ta kasar ta yi kira sau tari ga kasashen duniya da su aika da sojoji masu kiyaye zaman lafiya zuwa kasar; Amma 'yan gwagwarmayar kungiyar Islama sun yi Allah wadai da girke sojojin kowadanne kasashen ketare cikin yankin kasar, har sun ce za su mayar da sojojin kasashen ketare dake cikin yunkurin jibgewa a kasar a matsayin sojoji mahara. Lallai ba a manta ba, a watan Yuli na wanna shekara, jagoran " Kawancen kotu ta Islama" ya yi kira da a tayar da " yakin Jihadi" kan sojojin kasar Habasha magoya bayan gwamnatin rikon kwarya wadanda suke cikin yankin kasar Somaliya; Ban da wannan kuma, shawarwarin da aka yi tsakanin dakarun Islama da gwamnatin rikon kwarya a watan jiya ya sukurkuce, inda bangaren dakarun Islama ya ce wai sharadin farko na sake farfado da shawarwari shi ne janye sojojin Habasha daga kasar; Dadin dadawa, a ran 12 ga watan nan, " Kawancen kotu ta Islama" ya diba wa'adi kan sojojin kasar Habasha dake tsugunewa cikin yankin kasar Somaliya ,wato ke nan wajibi ne su janye jikinsu daga kasar Somaliya cikin mako daya, in ba haka ba,  dakarun Islama za su kai musu hari bisa babban mataki. To, a ran 19 ga wata da daddare wato sa'o'I biyu bayan wa'adin ya cika, dakarun Islama sun dauki matakin soja kan sansanoni biyu na ma'aikan soja masu yin horo na kasar Habasha, wadanda gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya ta kafa.

Jama'a masu saurare, abun mamaki shi ne daidai a ranar da fadan ya sake barkewa, sai shugaba Abdullahi Yusuf na gwamnatin rikon kwarya da shugaba Hassan Dahir Aweys na kungiyar dakarun Islama da kuma wakilin kungiyar tarayyar Turai Mr. Louis Michel sun yi shawarwari tsakaninsu, inda Mr. Michel ya sanar da cewa wai bangarorin biyu dukansu suka yi alkawarin daina yin nukura da juna da kuma sake komawa kan teburin shawarwari ba tare da kowane sharadi ba, ta yadda za a gano bakin zaren daidaita rikicin Somaliya; A nasa wajen, Mr. Aweys shi ma ya ce fadan da ya barke a wancan rana karamin abu ne da ya wakana ba zato ba tsammani kuma a cewarsa an riga an samu ra'ayi iri daya a gun shawarwarin.

To, ina " Ra'ayi iri daya" da aka samu? Ga shi cikin kwana biyu bayan wannan lokaci, an yi ta yin fada mai tsanani. Gwamnatin rikon kwarya da kuma kungiyar dakarun Islama suna zargin juna, kuma sassan biyu sun yi ta harba rokoki tare da yin amfani da bindigogin atileri a kan juna, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Domin gudun wannan masifa, mutane da yawa na kasar Somaliya sun tsira daga gidajensu zuwa sauran wurare. . ( Sani Wang )