Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-21 18:21:18    
Bayanin Gwamnatin kasar Sin kan zaman rayuwar mata da yara (babi daya)

cri

A ran 11 ga watan Oktoba na wannan shekara , an rufe taro na 6 na dukkan wakilai na Kwamitin Tsakiya na 16 na Jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Sin wanda aka shafe kwanaki 4 ana yin sa a nan birnin Beijing . Taron ya tatauna kuma ya zartas da " Kudurin da Kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminisanci ta kasar Sin ya tsayar kan wasu manyan matsaloli game da raya zaman al'umma mai jituwa ta kasar gurguzu" , kuma an tsai da manyan makasudai 9 da za a tabbatar da su zuwa shekarar 2020 , ciki har da raya aikin mata da yara da kyautata tsarin dokokin shari'a da rage bambamcin dake tsakanin birane da kauyuka kuma tsakanin shiyyoyi daban daban . A cikin shirinmu na yau za mu yi 'dan bayani kan kyautata zaman rayuwar mata da yara .

Me ya sa yanzu kasar Sin ta gabatar da maganar raya zaman al'umma mai jituwa ? Me Ya sa aka mai da wannan magana bisa matsayin wata sanarwa na tsarin ka'ida? To , bari mu tabo magana kan wadannan matsalolin .

Tun shekarar 1978 zuwa yanzu , an riga an shafe shekaru 28 ana yin gyare-gyaren tattalin arzikin kasar Sin , kuma an samu manyan nasarorin da suka jawo hankulan kasashen duniya ko a wajen karuwar tattalin arziki ko kuwa a wajen sauyawar tsarinsa

Jama'a masu sauraro , kasar Sin kasa ce mai tasowa wadda take da mafi yawan mutane a duniya . Yawan mata ya kai kimanin kashi 50 cikin 100 . Karfafa zaman daidaici da aikin mata ba kawai yana da muhimmanci ga yalwatuwar kasar Sin ba , har ma zai kawo tasirin musamman ga ci gaban 'dan Adam a duniya .

Kasar Sin za ta kara karfin kiyaye ikon mata da yara . Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labarin cewa , A ran 16 ga watan Janairu , wani jami'in Kungiyar kiyaye ikon mata da yara ta kasar Sin ya bayyana cewa , a wannan shekara kasar Sin za ta ci gaba da karfafa aikin wannan fanni wato za ta kara karfin kiyaye ikon mata da yara .

A Unguwar Haidian na birnin Beijing akwai wata makarantar musamman wadda take karbi yara masu karacin basira wato Makarantar firamare ta Peizhi . Wakilin Rediyon kasar Sin ya kai ziyara a wannan makarantar , inda ya gano cewa , a wannan makarantar akwai cikakkun kayayyakin koyarwa da isassun malamai masu koyarwa . Koyon ilmi da zaman yau da kullum na yaran ba su da bambanci bisa na daidaitattun yara . Liu Xuting , yaro mai karancin basira ya gaya wa wakilinmu cewa , yana jin dadi sosai a cikin makarantar .

Ya ce , kawunai da goggo masu yawa suna kula da ni . A nan ina farin ciki a kowace rana . A wajen koyon ilmi , malamai maza da mata suna kula da ni . Zan mai da hankali sosai kan karatu . A nan kasar Sin an kara mai da hankali kan tarbiyyar nakasassun yara kuma ana lura da su fiye da da . Wannan ya bayyana cewa , aikin da kasar Sin ta yi a wajen kiyaye ikon mata da yara ya kara karfi sosai . A cikin 'yan shekarun da suka shige , a nan kasar Sin daga shugabanni zuwa mutanen farar hula sun mai da muhimmanci kan kiyaye iko da moriyar yara da mara wadanda suke matsayi maras karfi . A gun taron aikin da Kungiyar kiyaye ikon mata da yara ta kasar Sin ta shirya a ran 16 ga watan Janairu a nan birnin Beijing , wakilinmu ya sami labarin cewa , wannan aikin ya sami ci gaba kwarai da gaske a cikin watan Nuwamba na shekarar 2006 da ya wuce ba da dadewa ba .