 Wakilin Rediyonmu ya sami labari cewa , a ran 19 ga watan nan a birnin Tripoli , hedkwatar kasar Lybia , Kotun Benghazi ta kasar ta yanke hukuncin kisa ga nas-nas mata guda 5 na kasar Balgaria da wani likitan Palasdinu sabo da laifin 'dura kwayoyin HIV masu hadasa cutar sida ga kananan yaran kasar Lybia da gangan .
A watan Mayu na shekarar 2004 , Kotun birnin Benghazi ta taba yanke hukuncin kisa ga wadannan mutane 6 . Babbar Kotun kasar Lybia ta bs da umurnin sake duba wannan hukunci . Wannan ne karo na biyu da Kotun birnin ta yanke musu hukuncin kisa . Gwamnatin Kasar Balgaria da Kungiyar Tarayyar kasashen Turai da kasar Amurka sun nuna adawarsu ga hukuncin .
Lamarin yaduwar kwayoyin cutar sida a birninn Benghazi na kasar Lybia ya auku ne a karshen shekarar 1999 . A lokacin a wani asibiti mai sunan Fatah na birnin Benghazi dake gabashin kasar Lybia , yara 426 na kasar sun kamu da kwayoyin cutar sida . Yara 53 daga cikinsu sun mutu. Bisa binciken da aka yi , an ce , nas-nas mata guda 5 na kasar Balgaria wadanda suka zo wannan asibiti ba da dadewa ba da wani likitan Palasdinu , an tuhume su da 'dura kwayoyin HIV masu haddasa cutar sida da gangan .
Tun daga shekaru 80 na karnin da ya wuce ne , aka gano cutar sida . Sa'an nan kuma tana yaduwa da saurin gaske a duk duniya . Ya zuwa yau , cutar sida ya yi sanadiyyar mutuwar mutane miliyan 25 . Kungiyar kiwon lafiya ta duniya da Hukumar shirin cutar sida ta Majalisar Dinkin duniya sun kiyasta cewa , yanzu a duk duniya mutane kimanin miliyan 40 sun harbe kwayoyin cutar sida . Ko da ya ke a wasu kasashen Caribbees da Afrika yawan mutanen da sukan kamu da kwayoyin cutar sida ya ragu , amma duk da haka kowace rana akwai mutane dubu 11 da suke mutuwa sabili da cutar .
Masana masu yawa sun bayyana cewa , a cikin shekaru 20 da suka shige , kokarin da kasashen duniya suke yi ya rage saurin yaduwar cutar sida , amma Aikin rigakafi da magance cutar Sida na duniya ya gamu da matsaloli masu yawa . Abin farin ciki ne wasu kasashe sun sami babban ci gaba a wajen magance cutar sida . Wani jami'in Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Lybia ya bayyana cewa , A lokacin da aka yi gwaje-gwajen maganin warkar da mutane masu fama da ciwon sida . Yanzu Wasu maganganun sun riga sun fito daga Dakunan gwajin kimiyya . Wasu kuma nan gaba kadan za su fito daga dakunan . Dukanninsu za su kawo alheri ga mutane masu fama da cutar Sida .
Sabon maganin Kwayoyin Tangcao maganin gargajiyar kasar Sin na farko ne wanda aka yi nazari a asibiti don yaki da cutar sida . Gwaje-gwaje sun shaida cewa , wanda ya hadiya maganin
kwayoyin Tangcao , sai jikinsa ya kyautu kuma lafiya ta sami sauki . Wato maganin yana da amfanin yaki da cutar sida kuma babu sauran illa da mugun tasiri .
Maganin gargajiyar kasar Sin mai suna Med mai yaki da cutar sida an riga an yi amfani da shi sau uku a asibitocin kasar Thailand . Sakamako ya bayyana cewa , wannan maganin ya iya kashe kwayoyin cutar sida , kuma ya iya kara abubuwan gina jiki . Sa'an nan kuma ba a ga illa da ya kawo ba . Ba kawai ana iya yin amfani da shi kadai ba , har ma a iya hade da shi da maganin kimiyyar Yamma don kara karfin magance cutar sida . Wani jami'in Kungiyar kiwon lafiya ta duniya ya bayyana cewa , a cikin 'yan shekarun da suka shige , likitocin kasashe daban daban na duniya sun ba da taimako sosai a cikin harkokin hana yaduwar ciwon sida . Musamman ma kasar Sin ta kai agaji sosai a wajen . Ya kamata su ci gaba da ba da amfaninsu a cikin famar yaki da cutar sida .
Bisa kididdigar da aka yi , an ce , yanzu yara wadanda suke da shekaru daga 13 zuwa 15 da haihuwa sun kai kashi 20 cikin 100. Kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta buga wani bayani cewa , hana yaduwar cutar sida a cikin yara da matasa aiki ne daya dake cikin muhimman ayyukan Kungiyar a nan gaba . A wannan fannin , gwamnatin kasar Sin tana mai da muhimmanci kwarai da gaske , kuma tana hada kanta da sauran kasashe don nazarin sababin magunguna masu yaki da cutar sida .(Ado )
|