Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-20 17:10:58    
Aikace-aikacen al'adun kasashen Afrika da aka yi a birnin Beijing

cri

Abubuwan da kuke saurara yanzu su ne kidan raye-rayen gargajiyar kasashen Afrika da daliban kasashen Afrika da ke karatu a kasar Sin suka nuna wa 'yan kallon kasar Sin a babban titin kasuwanci na yin tafiya da kafa kawai na Wangfujing da ke birnin Beijing, wasannin da daliban kasashen Afrika suka yi cikin himma da kwazo sun burge 'yan kallo sosai, mutane da yawa da ke wurin titin su ma sun shiga raye-rayensu. Bayan da wata 'yar kallo ta yi kallon wasannin, sai ta yi farin ciki tare da mamaki cewa,

Abin kyau ne gare ni, ya kamata za a kara shirya irin wadannan wasanni, wannan zai ba da taimako ga kara dankon zumuncin da ke tsakanin jama'ar Sin da jama'ar Afrika, a da ban taba kallon wasannin kasashen Afrika ba, sai yau ke nan, ina kaunar jama'ar Afrika sosai, a gaskiya dai ne jama'ar Sin da jama'ar kasashen Afrika suke iya shiga cikin zuciyarsu ya juna.

Wani dalibin kasar Nigeriya da ke karatu a jami'ar koyar da harsunan waje ta birnin Beijing Kelechi Ikonne ya bayyana cewa, yanzu yana nan yana kokarin koyon harshen Sinanci, kuma ya riga ya je yawon shakatawa a birane da yawa na kasar Sin, mutanen kasar Sin da na Afrika suna iya yada al'adunsu da kansu ta hanyar yin cudayar junansu. Ya bayyana cewa,

a kasar Nigeriya, da akwai mutanen Sin da yawansu ya kai dubu 20, suna magana da harshenmu, suna aiwatar da harkokin kasuwanci a kasarmu, suna son kasarmu sosai, a daidai da wannan kuma, dalibanmu da yawa suna koyon harshen Sinanci da sauran ilmi a kasar Sin, mun iya yin ma'amalar al'adunmu da kanmu a tsakaninmu, ina son kasar Sin fiye da sauran kasashen duniya, kasar Sin na da kyau sosai.

Kasar Sin da kasashen Afrika suna yin ma'amalar al'adu a tsakaninsu cikin dogon lokaci, al'adun kasashen Afrika da fasahohinsu sun burge mutanen kasar Sin da sauransu da suka taba zuwan kasashen Afrika ko yin aiki a can .

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, bisa albarkacin kara yin cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, ma'amalar al'adu a tsakaninsu sai kara karuwa, kuma mutane masu aikin sana'ar fasaha na gwamnati ko masu zaman kansu suna ta kara karuwar cudanya a tsakaninsu, bangarorin biyu sun taba shirya wasu manyan shagulgulan al'adu a tsakaninsu cikin hadin guiwa.

Direktan sashen fasaha na gidan baje koli na kasar Botswana Lesiga Phillip Segola ya bayyana cewa, a wajen masu aikin fasaha na kasarmu, abubuwan kasar Sin da yawa da muke cancantar koyo, kamar su fasahar yin zane-zane da dai sauransu, a sa'I daya kuma, daga zuwanmu a nan kasar Sin, aminanmu na kasar Sin za su iya kara fahimtar abubuwan kasashen Afrika da na kasar botswana, ta hakan, huldar da ke tsakanin aminai za ta iya kara karfi, a ganina, wannan na da muhimmanci sosai gare mu.

Mr Segola ya ci gaba da cewa, kasar Botswana da kasar Sin sun riga sun soma aiwatar da wani shirin yin ma'amalar al'adu a tsakaninsu, wato a ko wadanne shekaru hudu hudu, bangarorin biyu suke shirya manyan nune-nune da sauran aikace-aikacen al'adu a kasashen nan biyu bisa babban mataki, ya cika imani sosai ga raya da yin ma'amalar al'adu a tsakanin bangarorin biyu, kuma yana son sake zuwan kasar Sin a nan gaba.(Halima)