Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-20 08:36:36    
Liu Xiang ya ciyar da wasan tsalle-tsalle da guje-guje na Asiya gaba

cri

A gun taron wasannin Asiya da aka yi a birnin Doha na kasar Quatar,da zarar Liu Xiang,`dan wasa daga kasar Sin wanda shi ne zakaran gudun tsallake shinge na mita 110 na taron wasannin Olimpic kuma wanda ke rike da matsayin koli na wasan na duniya ya fito kan hanyar gudu ta filin wasan motsa jiki na Khalifa,sai a kullum ya jawo hankulan `yan wasan tsalle-tsalle da guje-guje da malaman wasa da kuma kafofin watsa labarai.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan Liu Xiang da gudumuwar da yake bai wa wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasashen Asiya.

A ran 11 ga wata,agogon wurin,Liu Xiang ya shiga gasa,a wannan rana da sassafe,babban malamin koyar da wasa na babbar kungiyar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ba ta lokacin aiki ba ta Hongkong Lin Weiqiang ya isa filin gasa tare da injin daukan video,yayin da Liu Xiang yake gudu,daga farko zuwa karshe,malamin wasa Lin ya rike dauka masa video,a sa`i daya kuma,ya canja ra`ayi kan fasahar wasa da Liu Xiang ke nunawa da abokinsa.Malamin wasa Lin Weiqiang ya gaya wa manema labaru cewa,nasarar da Liu Xiang ya samu ta canja ra`ayin mazauna Hongkong kan wasan tsalle-tsalle da guje-guje.Ya ce, `A Hongkong,ana iya ganin cewa,nasarar da Liu Xiang ya samu ya ciyar da wasan tsalle-tsalle da guje-guje.Dalilin da ya sa haka shi ne domin yanzu ana tsammanin cewa,lallai mutanen kasar Sin su ma suna iya wasan tsalle-tsalle da guje-guje sosai,saboda Liu Xiang daga kasar Sin ya riga ya zama zakaran duniya,shi ya sa yaran dake koyon wasan tsalle-tsalle da guje-guje a Hongkong suna kara karuwa a kwana a tashi.Amma a da ba haka ba ne,saboda haka ana iya cewar,Liu Xiang ya ingiza bunkasuwar wasan tsalle-tsalle da guje-guje a Hongkong.`

A gun taron wasannin Asiya,yara da yawan gaske sun je filin wasannin motsa jiki domin kallon gudun Liu Xiang,sun zo ne daga makarantar koyon wasanni ta Aspire dake birnin Doha na kasar Quatar.Musa shi ne daya daga cikinsu,yana koyon wasan gudun tsallake shinge na mita 110 na maza a makarantar,Liu Xiang shi ne abin koyinsa.Musa ya gaya mana cewa,  `Liu Xiang shi ne abin koyi na yawancin `yan wasa na makarantar Aspire,mun zo nan domin nuna masa goyon baya,dalilin da ya sa haka shi ne domin Liu Xiang ya kago matsayin kolin duniya musamman domin shi ne `dan Asiya.`

Musa ya ci gaba da cewa,nasarar da Liu Xiang ya samu ta bude wata kofa ga `yan wasa na Asiya,daga nan an gane cewar `yan wasa na kasashen Asiya su ma suna iya wasan tsalle-tsalle da guje-guje kamar yadda `yan wasa na sauran kasashen duniya ke yi.Yanzu Liu Xiang ya riga ya zama abin koyi na yara wadanda ke kaunar wasannin motsa jiki.

Hassan,`dan wasa daga kasar Malaysia wanda ya shiga mataki na farko na gasar gudun tsallake shinge na mita 110 a ran 11 ga wata ya ce,yana sanya matukar kokari domin zama Liu Xiang na biyu wato yana so ya zama sabon zakaran duniya.Ya gaya mana cewar,Liu Xiang shi ne `dan wasa mai kyau,bayan da ya kago sabon matsayin koli na duniya,mutanen kasashen duniya sun fara mai da hankali kan Asiya,wasan tsalle-tsalle da guje-guje na Asiya shi ma ya samu yalwatuwa,matsayin wasannin motsa jiki na Asiya ya dada daguwa a kai a kai.

Mataimakin direktan cibiyar kula da wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin kuma babban malamin koyar da wasa na kungiyar wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Sin Feng Shuyong yana ganin cewa,Liu Xiang ya sa mutanen kasashen duniya su kara mai da hankali kan wasan gudun tsallake shinge na mita 110,daga baya kuma matsayin wasan shi ma ya dagu daga dukkan fannoni.A Asiya kuwa,Liu Xiang ya sa `yan wasa su cike da imani,ya ce,  `A Asiya,Liu Xiang ya ba da babban taimako ga `yan wasa musamman wajen imani,wato mutanen kasashen Asiya sun fara cike da imani,sun canja ra`ayinsu na da,yanzu dai suna ganin cewa,`yan wasa na kasashen Asiya su ma suna iya wasan tsalle-tsalle da guje-guje sosai.Kodayake kila ne a wasu fannoni,suna kama baya,amma a ganina,idan `yan wasan Asiya su kara kyautata fasaharsu,to,za mu samu ci gaba a bayyane,za mu samu sabuwar nasara wajen wasan tsalle-tsalle da guje-guje.`(Jamila Zhou)