Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-20 08:34:25    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (14/12-20/12)

cri

Ran 15 ga wata,an rufe zama na 15 na taron wasannin Asiya a birnin Doha,babban birnin kasar Quatar,`yan wasa fiye da dubu goma da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 45 sun shiga wannan gaggarumin taron wasanni na Asiya,gaba daya sun samu lambobin zinariya 424.Bayan da aka kammala gasanni a cikin kwanaki 15 da suka shige,kasashe da shiyyoyi 26 sun samu lambobin zinariya,wadda a ciki kasar Sin ta samu lambobin zinariya 165 da na azurfa 88 da kuma na tagulla 63,wato lambobin zinariya da ta samu sun fi yawa,ban da wannan kuma,kasar Korea ta kudu da kasar Japan sun zama na biyu da na uku.Za a yi zama na 16 na taron wasannin Asiya a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin a shekarar 2010.

Ran 17 ga wata,kwamitin wasannin Olimpic na kasashen duniya da kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing sun zabi hotel biyu mafiya nagarta na Beijing da su zama hedkwatar ba da umurni na taron wasannin Olimpic na Beijing na shekarar 2008,wadannan hotel biyu su ne Beijing hotel da Guibinglou hotel wato Grand Hotel Beijing.A gun gasannin taron wasannin Olimpic na Beijing na shekarar 2008,muhimman jami`ai na kwamitin wasannin Olimpic na duniya da kwamitocin wasannin Olimpic na kasashe daban daban da shiyoyyi daban daban za su sauka a nan.

Daga ran 16 zuwa ran 17 ga wata,aka yi zagaye na karshe na gasar yawon kasa kasa ta sana`a ta shekarar 2006 ta hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tebur ta duniya a Hongkong,yankin musamman na kasar Sin,kungiyar `yan wasan kasar Sin ta samu zakaru na gasa tsakanin maza da gasa tsakanin maza da kuma mace da namiji da kuma mace da namiji,wanda a ciki `dan wasa daga kasar Sin Wang Hao ya lashe shahararren `dan wasa daga kasar Korea ta kudu Oh Sang Eun ya zama zakaran gasa tsakanin namiji.

Ran 16 ga wata,an kammala karo na karshe na babbar gasa ta ba da babbar kyauta ta wasan kankara salo-salo ta duniya a birnin St.Petersburg na kasar Rasha,`yan wasa daga kasar Sin Shen Xue da Zhao Hongbo sun samu lambawan na gasar wasan kankara salo-salo na mace da namiji da kuma mace da namiji. (Jamila Zhou)