Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-19 18:26:54    
Kasar Sin za ta kara yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi

cri

Ya zuwa karshen shekarar da muke ciki, za a kawo karshen lokacin wucin gadi bayan shigar kasar Sin cikin kungiyar cinikayya ta duniya, wato WTO. Bisa alkawarin da ta dauka lokacin shigarta cikin WTO, gaba daya ne kasar Sin za ta bude kasuwannin kudi da inshora. Sakamakon haka, aikin yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi da kasar Sin ke yi zai fuskanci sabon kalubale mai tsanani. Tun da haka, hukumar 'yan sanda da bankin tsakiya na kasar Sin sun bayyana cewa, za su dauki sabbin jerin matakai domin karfafuwar yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi.

A gun wani taron manema labaru da aka yi a ran 19 ga wata, madam Cai Yilian, mataimakiyar direktan hukumar yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi ta bankin jama'ar kasar Sin, wato bankin tsakiya na kasar Sin ta jaddada cewa, bayan shigowar bankuna masu jarin waje a kasar Sin, za su kuma dauki hakkin yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi kamar yadda bankunan kasar Sin suke yi. Madam Cai ta ce, "Bayan shigowar bankuna masu jarin waje a kasar Sin, hukumar sa ido kan sha'anin kudi ta kasar Sin za ta kuma sa ido a kan su kamar yadda take sa ido kan bankunan kasar Sin. Suna kuma da nauyin yin yaki da yunkurin halartar da kazamin kudi da ke wuyansu. Dole ne wadannan bankuna masu jarin waje su kafa tsarin sanin asalin bakinsu da tsarin ajiye takardu game da baki da takardu kan yadda baki suke yin ciniki ta banki. A waje daya kuma, dole ne a kafa tsarin ba da rahoto idan an yi shigi ko ficin kudade masu dimbin yawa daga banki a karo daya, ko banki ya yi shakkar cinikin kudi da aka yi."

Amma wannan jami'a wadda ke kula da aikin yin yaki da halaltar da kazamin kudi a bankin tsakiya na kasar Sin ta ce, yaya za a sa ido kan aikin yin yaki da halaltar da kazamin kudi a bankuna masu jarin waje, wannan wata tambaya ce da ke kasancewa a gaban bankin tsakiya na kasar Sin. Madam Cai ta ce, bankin tsakiya na kasar Sin zai kara yin hadin guiwa da takwarorinsa na kasashen waje domin yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi.

A da, ana yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi a cikin bankunan kasar Sin ne kawai, amma, yanzu masu laifuffuka da yawa suna halaltar da kazamin kudaden da suka samu bayan da suka yi sufurin kayayyaki cikin asiri ko suka yi fataucin miyagun kwayoyi ko suka ci hanci da rashawa. Yanzu tsarin bankuna ba hanya kadai da ake halaltar da kazamin kudi ba, ana kuma halaltar da kazamin kudi ta hanyoyin sayen gidaje da kayayyakin ado da kayayykin tarihi da dai makamatansu. Sabo da haka, tuni bankin tsakiya na kasar Sin ya hada kan hukumar 'yan sanda wajen yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi. A sakamakon hadin guiwar da aka yi a tsakaninsu, a shekarar da muke ciki, kasar Sin ta gano wasu manyan matsalolin halaltar da kazamin kudi da yawan kudadensu ya kai dalar Amurka kimanin biliyan 1.8. A shekara mai zuwa, za a kara yin irin wannan hadin guiwa a tsakaninsu. Madam Han Hao, mataimakiyar direktan hukumar yin awon gaba kan laifuffukan da suka jibinci harkokin tattalin arziki a ma'aikatar tsaron zaman lafiyar jama'a ta kasar Sin ta bayyana cewa, "A shekara mai zuwa, ma'aikatar tsaron zaman lafiyar jama'a ta kasar Sin da bankin tsakiya na kasar Sin za su kara yin hadin guiwa, kuma za su yi kwaskwarima kan tsarin binciken masu laifuffukan da suka jibinci harkokin kudi."

A waje daya kuma, tun daga ran 1 ga watan Janairu na shekara mai zuwa, za a soma aiwatar da "Dokar yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi" a kasar Sin. Ko shakka babu, wannan doka za ta bayar da muhimmiyar gudummawa kan aikin yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi. Bisa ka'idojin da aka tsara a cikin wannan doka, za a kafa tsarin sa ido kan yunkurin halaltar da kazamin kudi tare da kafuwar hukumomin yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi a bankuna da hukumomin kudi. Bugu da kari kuma, za a aiwatar da manufofi da matakan yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi da yawancin kasashen duniya suke dauka a kasar Sin domin hana fitar da kazamin kudi zuwa kasashen waje. Madam Han Hao ta ce, "An zartas da 'Dokar yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi' a zauren zaunannen kwamitin majalisar dokokin kasar Sin. Tabbas ne wannan doka za ta ciyar da aikin yin yaki da yunkurin halaltar da kazamin kudi gaba." (Sanusi Chen)