Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-19 17:12:30    
Babban dutse na Qingchengshan da madatsar ruwa ta Dujiangyan

cri

Jama'a masu sauraro, muna muku godiya da sauraren shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici wato 'Garin Panda, lardin Sihuan'. A cikin shirinmu na yau, za mu ziyarci babban dutse na Qingchengshan da kuma madatsar ruwa ta Dujiangyan, wadanda ke cikin takardar sunayen wuraren tarihi na al'adu na duniya. Kafin mu soma shirinmu na yau, gi tambayoyi 2 da muka shirya muku, da farko ko an mayar da babban dutse na Qingchengshan tamkar mafari na addinin Taoism? Na biyu kuma, yaushe ne aka gina madatsar ruwa ta Dujiangyan?

Babban dutse na Qingchengshan yana kusa da birnin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan na kasar Sin. Da zarar ka shiga cikin kofar wannan babban dutse, sai ka fahimci cewa, an fi samun kwanciyar hankali a nan. Dogayen bishiyoyi suna tsayawa a gefunan hanya, suna da yalwa sosai. Rafuka suna gudana bisa kwaloluwa masu wandar-wandar, ruwan da ke fantsama kan ganyayen ciyayi yana walkiya. Hazo yana tafiya a cikin babban dutsen, in an kara isa kan dutse, hazon ya kara yawa.(music 1)

Babban dutsen Qingchengshan na daya daga cikin muhimman wuraren da aka fara yada addinin Taoism na kasar Sin. Ra'ayin da addinin Taoism ke tsayawa a kai shi ne yin zaman jituwa a tsakanin dan Adam da muhalli. Watakila ne yau da shekaru fiye da 1800 da suka wuce, mai kafa wannan addini ya zabi babban dutse na Qingchengshan, ya fara nazarin addinin Taoism saboda kwanciyar hankali a nan. Bayan kafuwarsa, addinin Taoism ya yi suna dogon lokaci yana ba da babban tasiri a kasar Sin har ma a duk Asiya ta Gabas. Har zuwa yanzu masu bin addinin Taosim fiye da 100 suna rike da addinin a tsanake a nan.

Cikakkun gidajen ibada na addinin Taoism da dama da wuraren tarihi da ke kasancewa a babban dutse na Qingchengshan sun sanya mutane su kara fahimtar ainihin addinin Taoism. Yawancin gidajen ibada na addinin Taoism da dakuna da hasumiyoyi suna boye a tsakanin bishiyoyi masu yalwa, shi ya sa babban dutsen da bishiyoyi da duwatsu da kuma rafuka da wadannan gine-gine sun zama abu daya.

A gaskiya kuma, masu yawon shakatawa da yawa ba su san cewa, an fi samun kwanciyar hankali da tsabta a bayan babban dutsen Qingchengshan ba. An fi jin dadi saboda taba muhalli. Tsohon garin Taian da ke cikin kwarin bayan babban dutse na Qingchengshan wuri ne mai kyau wajen yin rintsa a nan.(music 3)

A cikin garin Taian mai tsabta, kananan rafuka sun ratsa ko wace unguwa da ko wane daki. Ya fi kyau a yi yawo a cikin irin wannan gari ba tare da sa takalma ba. A gefunan hanyoyin da aka shimfida da duwatsu, akwai wasu kantuna, inda ake sayar da kayan lambu da kuma giyar da aka yi a gida.

Zama a kujarun da aka yi da gorori tare da shan shayi da kuma kallon hazo da hayaki da ke cikin babban dutsen ya kan faranta wa mutane rayuka sosai.

Wani shahararren wurin shakatawa da ke kusa da babban dutse na Qingchengshan shi ne madatsar ruwa ta Dujiangyan, wadda ginin yin amfani da ruwa ne mafi tsufa a duk duniya har zuwa yanzu.

Yau da shekaru fiye da dubu 2 da suka shige, wani jami'in wurin wai shi Li Bing ya jagoranci fararen hula wajen gina wannan madatsar ruwa a sashen tsakiya na kogin Minjiang. A cikin dukan tsoffin gine-ginen yin amfani da ruwa da suka shahara a duk duniya, sai madatsar ruwa ta Dujiangyan kawai har zuwa yanzu ake yin amfani da ita.

An ce, kafin gina madatsar ruwa ta Dujiangyan, ruwa ya gudana daga kan manyan duwatsu, a kan samu ambaliyar ruwa a lokacin bazara da na zafi. Madatsar ruwa ta Dujiangyan ya raba kogin Minjiang zuwa kashi 2, wato na gida da na waje. Kogin Mingjiang na gida ya taka rawa a fannin yin ban ruwa, kogin Minjiang na waje kuma ya iya rage ambaliya.

Ken Boyd, mai yawon shakatawa na kasar Amurka, ya nuna babban yabo kan zane mai kyau na madatsar ruwa ta Dujiangyan da kuma mutanen Sin masu dabara na zamanin da. Ya ce, (murya ta 6, Ken)

'Na ji mamaki sosai saboda an gina wannan madatsar ruwa yau da shekaru fiye da dubu 2 da suka wuce. Ta iya sarrafa ruwa yadda ya kamata. A lokacin fari, An samar da isasshen ruwa wajen yin ban ruwa, manoma sun ci gajiya. A lokacin damina kuma, ta iya kubutar da birnin daga ambaliyar ruwa.'

Wasu mutane suna cewa, babban dalilin da ya sa akwai wuraren tarihi da wurare masu ni'ima masu yawa haka a lardin Sichuan shi ne domin an gina madatsar ruwa ta Dujiangyan. Jama'a masu sauraro, yaya ra'ayoyinku?

To, kafin mu kawo karshen shirinmu na yau, bari mu maimaita tambayoyin da muka shirya muku, da farko ko an mayar da babban dutse na Qingchengshan tamkar mafari na addinin Taoism? Na biyu kuma, yaushe ne aka gina madatsar ruwa ta Dujiangyan?