Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-19 17:11:51    
Dakin nune-nunen tsoffin kayayyaki na Shanghai

cri

A cikin dakin nune-nunen tsoffin kayayyaki na Shanghai da aka gina shi a shekara ta 1952, ana nuna kayayyakin al'adu fiye da 120,000, wadanda suka hada da kayayyakin da aka yi da tagulla da fadi-ka-mutu da rubutu da zane-zane da kayayyakin da aka shafe su da fenti mai kyalkyali da tsabar kudi da dai sauransu. Wannan dakin nune-nunen tsoffin kayayyaki ya yi suna ne saboda kayayyakin da aka yi da tagulla. A cikin wani daki mai fadin murabba'in mita 1,200, ana ajiye kyawawan kayayyakin tagulla fiye da 400, wadanda suka nuna ci gaban zaman al'ummar kasar Sin tun daga karni na 18 kafin haihuwar Annabi Isa zuwa karni na 3 kafin haihuwar Annabi Isa.

Hakazalika ana nuna mutum-mutumi fiye da 120 na zamanin da da kuma tumbura fiye 500 na zamanin da, wadanda suka hada da mutum-mutumin katako masu launuka na zamanin daular Zhanguo, wato tun daga shekara ta 475 kafin haihuwar Annabi Isa zuwa ta 221 kafin haihuwar Annabi Isa, da mutum-mutumin Buddha na zamanin daular Beiwei, wato tun daga shekara ta 386 zuwa ta 534, da kuma mutum-mutumin tukwane na dawaki da na sojoji na zamanin daular Tang, wato tun daga shekara ta 618 zuwa ta 907.

Ban da wannan kuma, masu yawon shakatawa suna iya ganin kayayyakin daki sama da 100 da aka yi a zamanin daular Ming da Qing, inda suka ji kamar yadda suke cikin wani lambu ko kuma wani babban gida irin na salon kasar Sin.

A cikin dakin nune-nunen tsabobin kudade, masu yawon shakatawa sun ji mamaki da ganin tsabobin kudade fiye da dubu 7, wadanda aka kera su da tagulla da zinariya da karfe da jan karfe. Dukan tsabobin kudade sun bayyana tarihin bunkasuwar aikin kerar tsabobin kudade ta kasar Sin.

Bugu da kari kuma akwai littattafai sama da 200,000 game da fasaha da tarihi na kasar Sin a cikin dakin nune-nunen tsoffin kayayyaki na Shanghai. Dakin ajiye kayayyakin tarihin nan ya kuma fito da sashen nazarin tsoffin kayayyaki don kula da ayyukan nazari da tonon tsoffin kayayyaki a wuraren da aka tono su. Har zuwa yanzu, wannan sashe ya ci nasarar tonon wuraren tarihi 27 a cikin shekaru 20 da suka wuce.