Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-18 17:56:48    
Takaitaccen bayani game da kabilar Pumi

cri

Yawancin mutanen kabilar Pumi suna da zama a gandumomin Lanpin da Lijiang da Weisi da Yongsheng da gandumar Ninglang ta kabilar Yi mai cin gashin kanta na lardin Yunnan, wasu kuma suna da zama a gandumar Muli ta kabilar Tibet mai cin gashin kanta da gandumar Yanyuan na lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2000, yawan mutanen kabilar Pumi ya kai kimanin dubu 33. Mutanen kabilar Pumi suna da yarensu, amma babu kalma yanzu.

Mutanen kabilar Pumi sun kware kan rera waka da taka rawa. A gun kowane irin biki, kamar su bikin aure ko bikin jana'izza, mutanen kabilar su kan rera wakoki iri iri na bayyana labaru. Bugu da kuma, suna rera wakoki game da soyayyar da ke kasancewa a tsakanin samari da 'yan mata. Sa'an nan kuma, mutanen kabilar Pumi sun fi son rera wakokin jama'a na kabila daban ta Naxi da na kabilar Han. Raye-rayen da suke takawa su kan bayyana yadda suke yin aikin gona da farauta da kuma yin sana'ar sassaka. Su kan taka rawa ne a karkashin kide-kiden da suka yi da kayan bushewa da sarewa.

Ko da yake mutanen kabilar Pumi suna da zama a wurare daban-daban, amma salon tufafin da maza suke sanya babu bambanci sosai. Amma kowa ya sani, mata sun fi son kyaun gani. Matan kabilar Pumi wadanda suke da zama a wurare daban-daban suna sanya tufafi iri iri.

Sa'an nan kuma, muhimmin abincin da mutanen kabilar Pumi suke ci shi ne masara, wasu lokaci suna cin shimkafa da alkama da dai sauransu. Bugu da kari kuma, mutanen kabilar Pumi suna yin amfani da katako suna gina gidajen da ked a soro da bene guda. Soro wurin kwana ne na tumaki da shanu, sai mutane suna zama a bene.

Mutanen kabilar Pumi wadanda suke da zama a gandumar Ninglang da ta Yongsheng, duriyoyi da dama suna zama tare. Amma a gandumar Lanping da ta Weisi, bayan da yara suka yi aure, sai a raba dukiyoyin iyaye ga dukkan yara maza. Bugu da kari kuma, a gandumar Ninglang, mata suna da matsayi a cikin gida, ba ma kawai mata suna da ikon gada dukiyoyin iyayensu ba, har ma ana girmama su kwarai lokacin da suke daidaita harkokin zaman al'umma.

Mutanen kabilar Pumi suna bin al'adar "Miji daya, mata daya", amma iyaye ne suke nema wa yaransu aure. Bugu da kari kuma, bayan da aka yi aure, ba dole ba ne amariya ta yi zama a gidan ango. Wannan kamar yadda mutanen kabilar Zhuang suke yi.

Haka nan kuma, yawancin mutanen kabilar Pumi suna girmamawa abubuwan al'ajabi. Wasu mutanen kabilar suna bin addinin Lama na jihar Tibet da addinin Dao, wani addinin gargajiya na kasar Sin.

To, jama'a masu sauraro, yanzu bari mu huta kadan. Daga baya, za mu ci gaba da shirinmu na yau na Kananan kabilun kasar Sin daga nan sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin. (Sanusi Chen)