Ran 15 ga wata, an kawo karshen tattaunawa a karo na farko da aka yi a kan harkokin tattalin arziki tsakanin kasashen Sin da Amurka bisa manyan tsare-tsare. A madadin shugabannin kasashensu, Madam Wu Yi, mataimakiyar firayim ministar kasar Sin da Mr Henry M. Paulson, ministan kudi na kasar Amurka suka shugabanci tattaunawar nan daya bayan daya. Bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi a kan babban jigon tattaunawar dangane da "hanyar bunkasuwa ta kasar Sin da manyan tsare-tsaren bunkasuwar tattalin arziki na kasar". Sa'an nan kuma gaba dayansu suna ganin cewa, ta hanyar tattaunawar, bangarorin biyu sun kara fahimtar juna da amincewa da juna, kuma sun aza harsashi mai kyau ga tataunawar da za su yi a nan gaba.
A gun taron manema labaru da aka shirya bayan tattaunawar, Malam Jin Renqing, ministan kudi na kasar Sin ya bayyana wasu ra'ayoyi iri daya da bangarorin biyu suka samu. Ya ce, "bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi kuma mai yaniki a tsakaninsu a kan batutuwan tattalin arziki na dogon lokaci kuma bisa manyan tsare-tsare. Sun nanata manufofinsu na bunkasuwar harkokin tattalin arzikin kasashen biyu cikin sauri da daidaituwa kuma a manyan fannoni. Alal misali yin kwaskwarima kan tsarin tsaida darajar kudin Sin Renminbi da kara yawan kudi da ake jiyewawa a bankunan kasar Amurka da sauransu."
Bayan haka Malam Jin Renqing ya kara da cewa, bangarorin biyu gaba daya sun amince da kiyaye ikon mallakar ilmi da kyau, da kara inganta tsarin dokoki, da kawar da tarnaki da suke yi wajen cinikayya da zuba jari, kuma suna ganin cewa, wannan yana da muhimmanci sosai ga kafa kasuwanni da ake yi takara da bude kofa.
Mataimakiyar firayim ministar kasar Sin Madam Wu Yi ya nuna yabo sosai ga tattaunawar da kasashen biyu suka yi a wannan gami. Ta ce, "ni da minista Paulson da ministocin kungiyoyin wakilan kasashen Sin da Amurka gaba daya muna ganin cewa, an sami sakamako mai kyau wajen yin tattaunawa ta karo na farko a tsakanin kasashen Sin da Amurka a kan harkokin tattalin arziki. Wannan zai ba da taimako ga bunkasa huldar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu, da huldar hadin kai mai yakini a tsakaninsu."
Madam Wu Yi ta kara da cewa, ta hanyar tattaunawar, bangarorin biyu sun kara fahimtar juna da aimcewa da juna. Sa'an nan sun sami wasu ra'ayoyi iri daya, amma ya kasance da wasu banbance-banbance a tsakaninsu. Muna iya fahimtar irin wadannan banbance-banbance, dalilin da ya sa haka, shi ne domin Sin da Amurka kasashe ne da suka sha banba sosai. Amurka kasa ce mai sukuni da ta fi girma a duniya, kasar Sin kuwa kasa ce mai tasowa da ta fi girma a duniya. Tushen tattalin arzikinsu da ra'ayoyinsu a kan tabi'u duk da dai sauransu sun sha banban sosai a tsakaninsu. Bangaren Sin yana fatan bangaroin Sin da Amurka za su iya samun bunkasuwa tare bisa ka'idojin girmama juna da zaman daidaici da moriyar juna da neman samun ra'ayoyi iri daya ba tare da yin la'akari da abubuwa da suka sha bamban a kansu ba.
Ministan kudi na kasar Amurka Paulson ya yarda da ra'ayoyin madam Wu Yi. Ya ce, "kasashen Sin da Amurka suna da moriyar tattalin arzkinsu iri daya a fannoni da dama, kuma muna da ra'ayoyi iri daya a kan batutuwa da yawa. Yayin da suka sami ra'ayi mai sha banban a tsakaninsu, za mu tattauna a kan abubuwa iri daya da za mu samu bisa ka'idar girmama juna. Mun yi tattaunawa a tsakaninsu cikin sahihanci, kuma mun sami sakamako mai kyau. Bangarorin biyu kullum suna neman hanyar da za su bi wajen daidaita matsaloli masu wahala." (Halilu)
|