Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-15 15:38:32    
Labarai game da wasannin motsa jiki na Olympic (1)

cri

Kuna sane da, cewa yau shekaru sama da 100 ke nan da aka gudanar da taron wasannin motsa jiki na farko na Olympic a shekarar 1896. Kuma taron wasannin Olympic na zamanin yau ya samu bunkasuwa har ya zama daya daga cikin manyan harkokin da suka fi yin tasiri ga zamantakewar al'umma da kuma janyo hankulan mutane. To, don me wani lamarin gasar wasannin motsa jiki ya iya yin babban tasiri kamar haka ? kuma wace irin hanya ce aka bi wajen gudanar da irin wannan gagarumin taron wasanni? Madam Sun Baoli, shahararriyar gwana a fannin wasannin Olympic kuma ta kasance falfesa ce daga Jami'ar wasannin motsa jiki ta Beijing, yau, za ta dan gutsura muku wani labari game da taron wasannin Olympic.

Madam Sun ta ce, yau da shekaru fiye da 100 ke nan da aka gudanar da taron wasannin motsa jiki na Olympic na zamanin yanzu, amma lallai lokutan nan kalilan ne idan an kwatanta su da na wasannin Olympic na can can zamanin da, wadanda suka dade har na tsawon shekaru sama da 1,100 ; Kodayake an gudanar da taron wasannin motsa jiki na Olympic na zamanin yanzu sau 28, amma kuwa uku daga cikinsu aka dakatar da yinsu sakamakon aukuwar babban yakin duniya ; Amma aka gudanar taron wasannin motsa jiki na Olympic na can can zamanin da har sau 293, wato ke nan aka iya nacewa ga gudanar da irin wannan gagarumar gasa sau daya cikin shekaru hudu. To, yaya ne aka gudanar da taron wasannin Olympic na can can zamanin da ? kuma saurin lokaci nawa ne 'yan wasan Olympic na can can zamanin da suka guda? Wadanne gasanni aka gudanar da su a wancan zamani ? kuma me ya sa aka dakatar da yinsu ba zato ba tsammani bayan da aka gudanar da su har na tsawon shekaru 1,100 ?

Madam Sun Baoli ta yi hasashen, cewa taro wasannin Olympic na zamanin yanzu ya kasance tamkar wani abu ne na al'adun zamantakewar al'umma, wanda aka haifar da shi a zamanin masana'antun jarin hujja ; amma sanadinsa shi ne taron wasannin motsa jiki na Olympic na can can zamanin da na tsohuwar Girka. An haifar da taron wasannin Olympic na can can zamanin da ne a shekara ta 776 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisalam, kuma aka dakatar da yinsa a shekara ta 394 bayan haihuwar Annabi Isa Alaihisalam, wato shekaru 1,169 ke nan da aka gudanar da irin wannan gasa har sau 293. Rahotannin tarihi sun bayyana, cewa aka gudanar da taron wasannin Olympic na can can zamanin da ne a wani karamin gari mai suna Olympia dake da nisan kilomita sama da 300 daga birnin Aden na yanzu. An bada wani labari a cikin wata da'awa, cewa wurin nan, wani wuri ne, inda gumaka iri daban daban na Girkasukan yi haduwa. A zahiri dai, wurin nan, wani wuri ne inda 'yan addini sukan yi sujadar ban girma. Ana kiran wurin nan a kan cewa ' Wurin Gumaka na Altis', wanda kuma tsawonsa daga gabas zuwa yamma ya kai mita 200, kuma fadinsa daga kudu zuwa arewa ya kai mita 175. Daga baya dai, aka gina wani filin wasan motsa jiki na musamman na Olympic na can can zamanin da a bakin wannan wurin gumaka. Fadin hanyar tsere ta wannan filin ya kai mita 32, inda 'yan wasa 20 suke iya yin gasa; kuma tsawon hanyar tseren ya kai mita 192, wadda aka gano ta bayan da aka kawo karshen babban yakin duniya na biyu.

Wasan gudu, muhimmin wasa ne dake cikin taron wasannin motsa jiki na Olympic na can can zamanin da. Yau da shekaru fiye da 2,000 da suka shige, an rubuta wassu babbaku kan tsaunin Girka, wato zauren taron wasannin Olympic na can can zamanin da a kan cewa: 'In kana so ka samu lafiyar jiki, to sai ku yi wasan gudu; In kana so ka zama mai wayo, to sai ka yi wasan gudu; kuma in kana so ka zama mai kyaun gani, to sai ka yi wasan gudu'.

Wasan gudu na taron wasannin Olympic na can can zamanin da yana da iri uku, wato na gajeren zango, da matsakaitan zango da kuma na dogon zango. Wasan gudu na dogon zango na tsohuwar Girka yana da nasaba da yaki. A wancan zamani, sharadin sadarwa bai kai a zo a gani ba. Domin mika wasiku da odoji, manzannin musamman na rundunar soja sun ga tilas ne su yi gudu na dogon zango tare da hawa kan duwatsu. Don haka ne, aka mayar da wasan gudu a matsayin ayyukan wasanni na Olympic.( Sani Wang )