Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-14 15:02:50    
Hukumomi da Cibiyoyi masu kula da harkokin Afrika na kasar Sin (kashi na hudu)

cri

Muna muku marahabin domin sauraren shirinmu na Me Ka sani game da kasar Sin . Wakilin Cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'umma ta kasar Sin ya bayyana cewa , shi kansa ya halarci wani taron da aka yi a ran 18 ga watan nan a nan birnin Beijing , jami'ai 18 masu kula da aikin noma na kasashen Afrika wadanda suke koyon ilmin fasahar kiyaye shuke-shuke a birnin sun bayyana cewa , Kasar Sin ta riga ta warware matsaloli masu yawa wadanda kasashen Afrika ke fuskanta yanzu . Wadannan fasahohi za su ba da taimako sosai ga kasashen Afrika . Suna fatan masanan kasar Sin za su je Afrika don yada fasahohinsu .

Hadin gwiwar aikin noma ya riga ya zama muhimmin fanni na hadin gwiwar tsakanin Sin da Afrika . A watan Janairu na wannan shekara , bayanin kan manufofin Afrika da kasar Sin ta bayar ya ce a bayyane , bangarori biyu za su mai da hankali sosai kan karfafa tsaron bunkasa gonakai da shuke-shuken aikin noma da fasahohin kiwon dabobi da tsaron abinci da sauran fannoni . Kasar Sin tana hadin gwiwa da mu'amalar aikin noma ta hanyoyi daban daban kuma matakai daban daban , ta yadda za a yi maganin matsalolin tsaron abinci na duniya .

Aikin noma muhimmin fanni ne da kasashen Afrika suka mai da hankali a kansa , kuma ya kai muhimmin matsayi a cikin tattalin arzikin galiban kasashen Afrika . Amma duk da haka saboda fasahohin aikin noma suke rashin ci gaba kuma a kan yi bala'o'I , shi ya sa a cikin mutane miliyan 860 akwai mutane miliyan 350 suna zaman rayuwa a karkashin layin talauci na duniya wato yawan kudin zaman yau da kullum a kowace rana bai kai dallar Amurka 1 ba .

Zhang Lijian , mataimakin shugaban Cibiyar Nazarin kimiyyar aikin noma ta kasar Sin ya ce , kasashen Afrika suna dogara bisa aikin noma . Kasar Sin kuma kasa ce ta aikin noma . Kasar Sin tana dogara bisa wadatattun fasahohin aikin noma kuma suna dawainiya da mutane na kashi 1 cikin kashi 4 na jimlar yawan mutanen duniya .

A cikin 'yan shekarun da suka wuce , gwamnatin kasar Sin ta samar da kudin rance mai gatanci kuma ta aike da masana zuwa kasashen Afrika don yin horon jami'an aikin noma . Yanzu jami'an gwamnatoci da 'yan fasaha fiye da 1000 wadanda suka zo daga kasashen Afrika fiye da 40 sun koyi ilmin fasahohin aikin noma a wadannan kwas na kara ilmin .

Ban da wannan kuma , tun daga shekarar 1996 , kasar Sin ta shiga shirin musamman da Hukumar aikin noma da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya kuma ta riga ta sa hannu kan yarjejeniyoyin tsakanin bangarori 3 da kasar Mauritania da kasar Ghana da kasasr Habasha da kasar Mali da kasasr Nigeria da kasar Saliyo . Yawan masanan fasahohin aikin noma da gwamnatin kasar Sin ta aike da su zuwa kasashen Afrika ya kai kusan 700 kuma sun zama misali a wajen hadin gwiwar aikin noma tsakanin Sin da Afrika .

Yanzu masanan aikin noma na kasar Sin suna koyar wa manoman kasar Afrika ta kudu yadda za su yi noman laiman kwadi da shinkafa . Kuma sun kafa sansanin shuka alkama a kasar Kamarun . Manoma masu yawa na Afrika sun bayyana cewa , kasar Sin tana kawo wa jama'ar Afrika hakikanin moriya . Suna fatan masanan kasar Sin da su yi aiki a kasashensu cikin dogon lokaci .

A cikin shirinmu na mako mai zuwa za mu ci gaba da karanta muku kashi na biyu na wannan bayani, wato za mu yi 'dan bayani kan Cibiyar nazari al'amuran Afrika na Jami'ar Beijing ta kasar Sin.(Ado)