Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-14 13:08:12    
An fi mai da hankali kan nahiyar Afirka a duk duniya

cri

Aminai makaunata, a da, idan an tabo magana kan Nahiyar Afrika, to abubuwan da akan tunar da su, su ne talauci, da yake-yake da kuma cututtuka. Amma a 'yan shekarun baya musamman ma a shekarar 2006, kasashe daban daban na duniya sun fi mayar da hankali kan nahiyar Afrika saboda ta kyautata yanayin tsaro da kuma farfado da tattalin arziki.

' Nan da shekaru goma masu zuwa, zaman walawa da kyakkyawar fata da kuma zaman lafiya za su samu babban ci gaba, wanda ba safai akan ga irinsa ba a da a duk Nahiyar Afrika. Jama'ar kasar Amurka sun hakkake, cewa ya kasance da babban boyayyen karfin samun bunkasuwa a Afrika', in ji shugaba GWB na Amurka yayin da yake bada lacca kan manufar da gwamnatin kasar take aiwatarwa a wannan shekara. Lallai mutane ba su manta ba, tuni yau da shekaru biyar da suka shige wato jim kadan bayan da Mr. Bush ya hau kan kujerar mulkin kasar, ya taba fadin cewa wai ' Nahiyar Afrika ba ta cikin da'irar moriya irin ta muhimman tsare-tsare ta kasar Amurka'. A watan Fabrairu na wannan shekara, tsohon sakataren kasar wato Mr.Donald Rumsfeld ya kai ziyara a kasashe uku na arewacin Afrika; Sa'annan kuma bangaren sojan Amurka yana gaggauta kafa hedkwatar Afrika domin yin tsaro a wasu muhimman wurare masu arzikin man fetur na Afrika. Duk wadannan dai sun shaida, cewa nahiyar Afrika na da muhimmancin gaske ga matsayin muhimman tsare-tsare na kasar Amurka game da duk duniya.

A daya gefen, shugaba Putin na kasar Rasha ya kai ziyara aiki har sau biyu a kasashen Afrika a wannan shekara. A yayin da yake yin ziyara a kasar Afrika ta Kudu, ya furta, cewa:

'Nahiyar Afrika na da muhimmancin gaske ga kasar Rasha domin ta gabatar mana da albarkataun halitta da kerarrun kayayyakin noma iri daban daban da kuma 'ya'yan itatuwa masu dadin ci. Babu tamtama wannan yana da amfani gare mu wajen kyautata huldar siyasa dake tsakaninua kasashen Afrika.'

A sa'i daya kuma, kasashen Japan da Korea ta Kudu na Asiya suna mai sha'awar yalwata dangantakar dake tsakaninsu da kasashen Afrika. Tsohon firaministan kasar Japan Mr. Koizumi Junichiro ya kai ziyara a kasashen Habasha da Ghana da kuma babban zauren kungiyar AU a karshen watan Afrilu na bana ; Shugaba Roh Moo Hyun na Korea ta Kudu ya kai ziyara a kasashe uku na Afrika a watan Febrairu na bana, sa'anann kasar ta shelanta cewa shekarar nan ' shekarar Afrika' ce ta Korea ta Kudu, ta kuma shirya zama na farko na taron tattaunawa kan hada kan Koriya ta Kudu da Afrika.

Ban da wannan kuma, ana ta kara hadin gwiwar tsakanin kasashen Nahiyar Amurka ta Kudu da na Afrika. An gudanar da taron koli na farko kan hadin gwiwar Afrika da Amurka ta Kudu a birnin Abuja na kasar Nigeria, inda aka cimma matsayi daya kan yadda za a kara yin hadin gwiwa tsakaninsu a fannoni daban daban'.

Game da wanan sabon tashen nuna sha'awa ga Afrika da aka tayar a duk duniya, wata kwararriya a hukumar nazarin harkokin yammacin Asiya da Afrika ta kasar Sin wato Madam He Wenping ta yi hasashen cewa, wani muhimmin dalilin da ya sa aka yi haka, shi ne aka samu kyakkyawan yanayin siyasa da bunkasuwar tattalin arziki a Nahiyar Afrika wadda kuma ta kara daga matsayinta a duniya.

Jama'a masu saurare, 'Taron koli kan hadin kan Sin da Afrika' da aka gudanar a watan jiya a nan Beijing ya kara yin yunkurin nuna sha'awa ga Afrika a duk duniya a wannan shekara. Shekarar nan, shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. A gun bikin bude taron kolin, shugaba Hu Jintao ya yi nuni da cewa : 'Yau, tushen zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya riga ya zauna sosai a cikin zukatan jama'ar bangarorin biyu. Har kullum mukan nuna sahihanci, da yin zaman daidai wa daida, da goyon bayan juna da kuma samun ci gaba tare.'( Sani Wang )