Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-13 16:25:18    
Sakonnin taya murna daga masu sauraro(2)

cri

A ran 3 ga watan Disamba na shekara ta 1941 ne, aka kafa gidan rediyon kasar Sin, wato CRI, wato daidai a ran 3 ga watan nan da muke ciki ke nan, CRI ya cika shekaru 65 da kafuwa. A kwanakin baya, bi da bi ne masu sauraronmu suka rubuto mana wasiku, inda suka taya mu murnar cika shekaru 65 da kafuwa.

Don taya mu murnar cika shekaru 65 da kafuwa, malam Hamza M Djibo, wanda ya fito daga birnin Niyame jamhuriyar Nijer, ya rubuto mana cewa, shekaru 65 na CRI shekaru ne da masu sauraro suka karu da su sosai musamman ga su jin harshen Hausa. Alal misali kamin kafuwar CRI Hausawanmu ba su da wani cikekken labarin yadda al'adu da halayan jama'ar Sin yake sai dai dan abinda ba a rasa ba ta hanyar finafinnan kasar amma yanzu muna da labarin yadda al'adun kabiloli daban daban yake a kasar Sin haka mun karu kwarai da sanin yadda siyasa da harakokin noma kiyon lafiya kimaya da fasaha suke gudana a kasar, don haka karuwar da muka yi da CRI a bace marar misulyuwa.

Sai kuma Sanusi Isah Dankaba sabon-layi Keffi jihar Nasarawa Nigeria, ya rubuto mana cewa, rediyon kasar Sin wani muhimmiyar tashar rediyo ce wadda take watsa shirye-shiryenta a duk fadin duniya a cikin harsuna sama da arba'in. A kwana A tashi wata rana jariri ango ne, yau ga shi allah ya nuna mana gidan rediyon kasar Sin ta cika shekaru sittin da biyar da kafawa wannan tasha mai farin jini. Ai ko ba a gwada ba liszafi ya fi karfin bakin kaza. Gidan rediyon kasar Sin ya shahara wajen watsa shirye shirye tare da ba da sahihan labaru dangane da ci gaban kasar Sin da yankin Asiya, kai har ma da duniya baki daya, a sabili da haka, wannan tasha ta samu karbuwa cikin sauri daga masu sauraronta a duk duniya. Akwai abubuwan ci gaba masu tarin yawa da wannan tashar rediyo ta samu tun daga kafa ta har zuwa yanzu, alal misali a cikin farkon wannan shekara, CRI ta kafa tashar FM ta farko a wata kasar waje a garin Nairobi ta kasar Kenya, kuma wani abu mai kama da wannan a cikin watan da ya wuce, CRI ta kafa wata tashar FM ta biyu a wata kasar waje a garin Vientiane na kasar Laos wanda shugaban kasar Sin Mr.Hu Jingtao ya bude da kansa. A ko da yaushe ra'ayina na tare da dogon hangen nesa a kan wannan tashar rediyo, nan gaba kadan cikin shekaru masu zuwa gidan rediyon kasar Sin zai zama gidan rediyo mafi girma a duniya.

Daga karshe inason in yi amfani da wannan dama in isar da sakon taya murna ga shugabannin wannan tashar rediyo mai farin jini a kan murnar cika shekaru sittin da biyar da kafa gidan rediyon kasar Sin.

Bayan haka, malam Salisu Muhammed Dawanau, da ke zaune a garki, Abuja, tarayyar Nijeriya, wanda ke sauraron shirye-shiryenmu a ko da yaushe, ya rubuto mana cewa, wannan labari ya samo asali ne daga ranar 3 ga watan Disamba na shekara ta 1941. A wancan lokaci, duniya tana cikin rudu da tashin hankali musamman sabo da yake-yake da mulkin mallaka da ake yi, da kuma tsananin duhun-kai da ke addabar wasu kasashe masu tasowa. Duk da halin da ake ciki na rashin tabbas, kasar Sin ta sadaukar da kanta wajen kafa wannan Gidan Rediyo da kuma shaida wa Duniya halin da ake ciki a kasar da kuma Nahiyar Asiya baki daya.

Kwanci-tashi, yau Allah Ya kawo mu wannan shekara ta 2006, yayin da CRI ta cika shekaru 65 da kafuwa.

A nan, ina so mu sani cewar, kafin yau, CRI din nan ta sha gwargwarmaya iri-iri, kuma ta yi juriya tamkar dan-Adam. Ta tunkari kalubale masu yawan gaske. Wadannan kalubale da juriya sun taimaka wa CRI sosai, yayin da a yau sai walwala da annashuwa ke gudana a harkokinta na yau da kullum. Ga sabbin sassa da rassa ta bude, ga ma'aikata masu yawa da kwazo, ga sabbin na'urorin hada labarai da tace su yadda za su dace da wannan zamani. Abin gwanin ban sha'awa!

Bugu da kari, CRI ta taimaka sosai wajen wayar da kai da kuma bude wa Duniya idanu dangane da sahihan abubuwan da suke faruwa a kasar Sin da Nahiyar Asiya baki daya. Ta taimaka wajen tallata kasar Sin ga Duniya, ta yadda yanzu kowa a Duniya ya san kasar da mutanenta da al'adunta da kuma irin tsarin mulkinta da dai sauransu.

A karshe, ina yi wa wannan Gidan Rediyo da kuma ma'aikatanta fatan alheri a kullum, musamman don su dada cimma nasarorinsu cikin sauki da kuma kwanciyar hankali.(Lubabatu)