Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-13 16:25:11    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(07/12-13/12)

cri
Ran 7 ga wata, a nan Beijing, babban injiniya kuma kakakin hedkwatar shugabancin ayyukan taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing Wu Jingjun ya bayyana cewa, za a kammala gina dukan filayen wasa da za a yi amfani da su a gun taron wasannin Olympic na shekara ta 2008 ta Beijing kafin karshen shekara ta 2007. Har zuwa yanzu, ana gina filayen wasa domin yin gasa guda 25 da filayen wasa domin yin horo guda 15 da kuma gine-ginen da abin ya shafa guda 5.

Ran 13 ga wata, ana cin gaba da taron wasannin motsa jiki na Asiya a birnin Doha, babban birnin kasar Qatar, har zuwa ran 12 ga wata, bisa agogon wurin, kungiyar wakilan 'yan wasan kasar Sin ta sami lambobin zinariya 137, ta ci gaba da zama ta farko a tsakanin kasashe da yankuna masu shiga wannan muhimmin taron wasannin motsa jiki. Kasar Korea ta Kudu ta zama ta biyu saboda samun lambobin zinariya 47, kasar Japan kuwa ta zama ta uku saboda samun lambobin zinariya 46.

Ran 6 ga wata, a babban zaurenta da ke birnin Zurich, Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA ta sanar da cewa, za a yi gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa a kasar Afirka ta Kudu tun daga ran 11 ga watan Yuni zuwa ran 11 ga watan Yuli na shekara ta 2010, sa'an nan kuma, za a rarraba kujerun shiga wannan gasa kamar yadda aka yi a gun gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta kasar Jamus a shekarar bana, wato kasashen Turai suna da kujaru 13, kasashen Afirka sun sami kujeru 5, kasashen Asiya suna da kujeru 4 da rabi, kasashen Amurka ta Kudu sun sami kujeru 4 da rabi, kasashen Amurka ta Tsakiya da ta Arewa da kuma na yankin tekun Caribbean sun sami kujeru 3 da rabi, kasashen nahiyar tekun Oceania sun sami rabin kujera, kasar Afirka ta Kudu kuma ta sami wata kujera a matsayin masaukin gasar.

Ran 2 zuwa 8 ga wannan wata, a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu, an yi gasar fid da gwani ta iyo ta nakasassu ta duniya ta shekarar 2006. Kasar Sin ta zama ta hudu domin samun lambobin zinariya 16, da na azurfa 17 da kuma na tagulla 10 a cikin jerin sunayen kasashe da yankuna ta fuskar lambobin yabo, ta kuma karya matsayin bajimta na duniya a cikin gasanni 11.(Tasallah)