Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-13 16:23:09    
Wani mai yin zane-zane na zamanin yau na kasar Sin mai suna Wan Jiyuan

cri

Mr Wan Jiyuan shi ne mai yin zane-zanen fenti da ke da halayen musamman , ayyukan gwamnati na yau da kullum na da yawan gaske gare shi, amma yana kishin yin zane-zane sosai da sosai. Ya je yawon shakatawa a duk duniya, kuma ya yi zane-zane da yawa don tunawa da abubuwan da ya ji ko ya gani a kowace rana. Halayen musamman na kasashe daban daban da ya bayyana su a kan zane-zanensa ya burge mutane da yawa, ya zuwa yanzu, ya riga ya yi nune-nunen zane-zanensa a gidan baje kolin kayayyakin fasahohin kasar Sin har sau biyu, ya ce yana da burin cimma zaman gobe.

In ka bude internet dangane da Wan Jiyuan, sai ka iya samun labaru da yawa dangane da shi, da akwai wani bayanin da wani mai yin sharhi kan kayayyakin fasahohi na kasashen yamma mai suna Jonathan Thonson ya yi sharhi da cewa, Mr Wan Jiyuan shi ne wani mai son yawon shakatawa da ke da tsayayyar niyyar yin abubuwa, ta hanyar yin amfani da alkalamin zane-zane ne ya yi zane-zane kan tafiye-tafiyen da ya yi don neman labarun duniya. Wani bayani daban da aka rubuta ya bayyana cewa, Mr Wan Jiyuan shi ne mai yin zane-zane da ke da sha'awa sosai ga sabbin abubuwa da sabbin halayen musamman da ake ciki da sabbin rukunonin mutane, ayyukan wurjanjan da ya yi cikin taurin kai sun wuce tsammanin da mutane suka yi. Game da wadannan sharhohi, Mr Wan Jiyuan ya bayyana cewa, a dukan lokatan da na tafi sauran kasashe, dole ne na yi tafiya tare da zawwatin yin zane-zane da akwatin ajiye kayayyakin yin zane-zane, a gaskiya dai ne na ji cewa, yin zane-zane ya riga ya zama bukatar da nake yi dole. An ce , tabbas ne wannan ya kawo gajiya sosai gare ni, amma na ce, in ban yi zane ?zane ba, to tabbas ne zan yi gajiya sosai., kuma na ji cewa, zane-zanen fenti sun riga sun zama wani kashi da ke cikin zaman rayuwata.

Mr Wan Jiyuna shi ne manajan cibiyar nuna kayayyakin fasaha da kasashen waje na kasar Sin, yana da shekaru 50 da haihuwa, amma a idon sauran mutane, shi ne saurayi ne da ke da kuzari sosai. Ya ce, burinsa daya kawai, wato yin zane-zane.

An haifi Wan Jiyuan a shekarar 1953 a wani karamin gari da ke da dogon tarihi na lardin Jangxi da ke kudancin kasar Sin. A shekarar 1972, Mr Wan Jiyuan ya koyi ilmin zane-zane a wata jami'a, bayan saukarsa daga karatu, sai ya sami wani aikin yi a wani gidan baje koli na lardin Jangxi. Sa'anan kuma , an kafa wata hukumar rubuce-rubuce da zane-zane ta lardin Jiangxi, Mr Wan Jiyuan ya zama mai yin zane-zane na musamman na hukumar, a wajensa, manyan ayyuka su ne yin zane-zanen fenti, daga nan ya riga ya yi suna sosai a rukunonin yin zane-zane na kasar Sin.

A shekarar 1989, Mr Wan Jiyuan ya zo nan birnin Beijing, ya sami aikin yi a cibiyar nuna kayayyakin fasaha da kasashen waje ta kasar Sin . Kodayake harkokin hukumar na da yawa gare shi, amma bai bari aikin yin zane-zane ba.

A kwana a tashi, Mr Wan Jiyuan ya tattara zane-zanensa da yawa, sai a shekarar 2001 ya yi nunin zane-zanensa a gidan baje kolin kayayyakin fasaha na kasar Sin, yawan zane-zanen da ya nuna ya kai 60 ko fiye da ya zabo su daga daruruwan zane-zanensa. Mr Wan Jiyuan ya bayana cewa, na yi daruruwan zane-zane a lokutan bayan aikina ne, wato a lokacin da sauran mutane suke hutawa, sai na yi zane-zane kawai, na ji cewa, lokacin yin zane-zane lokaci ne da na yi farin ciki sosai. Ya kara da cewa, na riga na tsara wani babban shiri, wato zan yi wasu zane-zanen da ke da halayen musamman na kasar Sin da sauri, Ina tsammani cewa, za a iya ganin fitowar da wani Wan Jiyuan da ke da bambanci da na yanzu.(Halima)